Yadda Abdulaziz Yari ya hada-kai da Akanta-Janar da wasu, aka wawuri kudin jihohi 9

Yadda Abdulaziz Yari ya hada-kai da Akanta-Janar da wasu, aka wawuri kudin jihohi 9

  • Ana tunanin Abdulaziz Yari ya samu kaso daga cikin kudin da ake zargin AGF ya yi sama da su
  • EFCC ta na binciken Ahmed Idris a kan wawurar N84bn daga cikin dukiyar jihohi masu danyen mai
  • Ana cewa Yari ya samu kudin zuwa Umrah, sannan wasu ma’aikatan RMAFC sun yagi rabonsu

Abuja - Jaridar Premium Times ta fitar da wani rahoto da ya yi bayanin zargin alakar tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari da Akanta-Janar.

Binciken da hukumar EFCC take yi ya bankado wasu akalla $700, 000 da Yari ya kashe daga cikin Naira biliyan 20 da ya karba wajen zuwa kasar Saudi Arabia.

Rahoton ya ce babban ‘dan siyasar ya karbi wadannan makudan kudi ne, ya tafi Umrah da su. Yari ya dauki hadimansa zuwa ketare inda aka kashe kudin.

Wani wanda ya san halin da ake ciki, ya shaidawa jaridar cewa wadannan kudi da aka wawura su na cikin 13% da ake warewa jihohin da ke da arzikin mai.

Kudin jihohi masu danyen mai

A maimakon Ahmed Idris ya biya wadannan jihohi tara hakkokinsu, sai ya ba darektan Westgate Projects Limited, Gbenga Akindele aikin Naira biliyan 84.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan bincike na EFCC ya nuna Idris ya hada-kai da Yari, da wasu ma’aikatan hukumar kason albashi da arzikin kasa na RMAFC wajen karkatar da kudin.

Tsohon Gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari
Shugaba Buhari da Tsohon Gwamnan jihar Zamfara Hoto: encomium.ng
Asali: UGC

Haka zalika babban Akantan na gwamnatin tarayya ya samu hadin-gwiwar wasu ma’aikata daga wadannan jihohi wajen yin kashe mu raba da sunan aiki.

An yi kashe-mu-raba

Shi wannan Akindele ya karbi N84bn na aikin bogi da ya yi, shi kuma ya shiga rabo. Jaridar ta yi yunkurin tuntubar Darektan kamfanin, amma ba a dace ba.

Zargin da ake yi shi ne Akindele ya lamushe 1% na kudin aikin, sai Yari ya karbi N20bn, ma’aikatan RMAFC da aka hada-kai da su, suka samu N16bn.

Sauran ma’aikatan jihohin da aka yi wa wannan barna sun samu kasonsu a rabon da aka yi.

Shi dai Yari ya karbi na sa kason ta hannun Anthony Yaro, wanda yake da alaka da Finex Professionals Services, ana tunanin Yari yake yi wa aiki.

Yari da AGF sun koma gida

Ku na da rahoto ana zargin akwai hannun Abdulaziz Yari a Naira biliyan 84 da ake zargin Akanta-Janar, Malam Ahmed Idris ya yi sama da fadi da su.

Sababbin bayanan da aka samu sun tabbatar da cewa Alhaji Abdulaziz Yari ya bar hannun EFCC. Shi ma AGF ya koma wajen iyalinsa bayan ya samu beli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel