Bayan janyewa Gwamnan Bauchi, an mayar da shi kujerarsa ta Sakataren Gwamnati

Bayan janyewa Gwamnan Bauchi, an mayar da shi kujerarsa ta Sakataren Gwamnati

  • An sake nada Barista Ibrahim Muhammad Kashim matsayin sakataren gwamnan jihar Bauchi
  • An nada lauyan ne bayan janyewe daga zaben gwamnan jihar duk da ya lashe zaben fidda gwani
  • Barista Kashim ya ce yan fasa takara a zaben jihar kuma ya janye, yanzu za'a sake saboda zaben fidda gwani

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Bauchi - Bayan janyewa daga takarar kujerar Gwamnan jihar Bauchi, an mayar da Ibrahim Kashim kujerarsa ta Sakataren gwamnatin jihar Bauchi.

Mai magana da yawun gwamnan jihar, Mukhtar Gidado, a jawabin da ya fitar ranar Alhamis a garin Bauchi.

Ya bayyana cewa Gwamna Bala Muhammad ya mayar da Kashim kujerarsa ne saboda mutum ne mai gaskiya kuma mai kwarewan gaske.

A cewarsa:

"Gwamna Bala Mohammed (Kauran Bauchi) ya amince da sake nada Barista Ibrahim Muhammad Kashim matsayin sakataren gwamnan jihar."

Kara karanta wannan

Tsohon dan takara a PDP ya lashe tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour

"An sake nadashi ne saboda biyayyarsa, gaskiyarsa da kuma kwarewa wajen gudanar da ayyukansa."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamnan Bauchi
Bayan janyewa Gwamnan Bauchi, an mayar da shi kujerarsa ta Sakataren Gwamnati Hoto: Kauran Bauchi Media TV
Asali: Twitter

Wanda ya lashe zaben fiddan gwanin Gwamnan Bauchi ya ce ya fasa baya so

Jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) a jihar Bauchi za ta gudanar da sabon zaben fidda gwanin yan takaran Gwamna sakamakon janyewan Kassin Ibrahim Mohammed, wanda ya lashe zaben.

Kakakin jam'iyyar PDP na jihar Bauchi, Alhaji Yayanuwa Zainabari, ya bayyana a hirarsa da Leadership cewa Kassim da kansa ya janye daga takarar.

A cewarsa, za'a gudanar da sabon zaben fidda gwani ranar Asabar.

Kassin, wanda yake tsohon sakataren gwamnatin jihar ya janyewa maigidansa, Gwamna Bala Mohammed AbdulKadir.

Wannan ya biyo bayan shan kaye da Gwamnan yayi a takarar tikitin kujerar shugaban kasa da yayi ranar Asabar da ta gabata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel