Da dumi: Wanda ya lashe zaben fiddan gwanin Gwamnan Bauchi ya ce ya fasa baya so

Da dumi: Wanda ya lashe zaben fiddan gwanin Gwamnan Bauchi ya ce ya fasa baya so

Jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) a jihar Bauchi za ta gudanar da sabon zaben fidda gwanin yan takaran Gwamna sakamakon janyewan Kassin Ibrahim Mohammed, wanda ya lashe zaben.

Kakakin jam'iyyar PDP na jihar Bauchi, Alhaji Yayanuwa Zainabari, ya bayyana a hirarsa da Leadership cewa Kassim da kansa ya janye daga takarar.

A cewarsa, za'a gudanar da sabon zaben fidda gwani ranar Asabar.

Kassin, wanda yake tsohon sakataren gwamnatin jihar ya janyewa maigidansa, Gwamna Bala Mohammed AbdulKadir.

Wannan ya biyo bayan shan kaye da Gwamnan yayi a takarar tikitin kujerar shugaban kasa da yayi ranar Asabar da ta gabata.

Bala ya samu kuri'u 20 inda Atiku wanda ya lashe zaben ya samu kuri'u 371.

Kara karanta wannan

Dan takarar shugaban kasa ya tono sirri: Ba dan ni ba da Buhari ya sha kaye a zaben 2015

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kashim
Da dumi: Wanda ya lashe zaben fiddan gwanin Gwamnan Bauchi ya janyewa Bala Mohammad Hoto: Premium TImes
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Online view pixel