Dattijo mai goyon bayan Atiku ya yanke jiki ya fadi ana tsaka da shagalin mika wa Atiku satifiket din takara

Dattijo mai goyon bayan Atiku ya yanke jiki ya fadi ana tsaka da shagalin mika wa Atiku satifiket din takara

  • Wani magoyi bayan 'dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya yanke jiki ya fadi a sakateriyar jam'iyyar a Wuse Zone 5 dake a Abuja a ranar Laraba
  • Mutumin ya kasa jure cunkoson da ke dakin taron mika takardar shaidar dawowar 'dan takarar jam'iyyar inda ya fadi warwas yayin da ya yi kokarin fita waje
  • Taron ya kunsa 'yan jam'iyyar da dama, magoya bayan dan takarar shugaban kasar da kuma amintattun jam'iyyar wadanda suka halarci taron fiye da yadda ake tsammani

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Wani magoyi bayan 'dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, wanda ba a riga an gano ko waye ba ya yanke jiki ya fadi a sakateriyar jam'iyyar a Wuse Zone 5 dake Abuja a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

2023: Atiku ya nemi hadin kan Wike, Saraki da sauran jiga-jigan PDP don lallasa APC

Mutumin ya rasa inda kansa yake ne a bikin da jam'iyyar ta shirya na damka takardar komen takara ga 'dan takarar shugaban kasar.

Dattijo mai goyon bayan Atiku ya yanke jiki ya fadi ana tsaka da shagalin mika wa Atiku satifiket din takara
Dattijo mai goyon bayan Atiku ya yanke jiki ya fadi ana tsaka da shagalin mika wa Atiku satifiket din takara. Hoto dga dailytrust.com
Asali: UGC

Dattijon ya kasa jure cunkoson da ke cikin dakin taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) na sakateriyar jam'iyyar ta kasa, wacce ta cika makil da dandazon da amintattu da magoya bayan jam'iyyar.

Duk iya kokarin da mashirya taron suka yi don ganin an rage cunkoson jama'an da suka zo don halartar taron, hakan ya ci tura, Daily Trust ta ruwaito.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ko na'urar sanyaya wurin bata iya bada iska yadda ya dace ba wanda ya yi sanadiyyar tsanantar zafi da tsananin gumi ga wadanda suke wurin.

Duk iya rokon da shugaban taron ga kungiyoyin magoya baya da sauran mabiya yayi kan su fita daga dakin taron NEC bai yi amfani ba.

Kara karanta wannan

Dan takarar APC: Abu mai sauki ne na lallasa Atiku a zaben 2023, a bani tikiti kawai

An kara kusan awa daya a kan taron, wanda aka yi niyyar gabatarwa karfe 12:00 rana, wanda ya bar 'yan jam'iyyar da dama, magoya baya da amintattun jam'iyyar cikin yanayin rashin jindadi.

Ba tare da iya jure yanayin da ya tsinci kansa ba, mutumin wanda ya yi kokarin fita daga dakin taron, sai ya yanke jiki ya fadi.

Lamarin ya jefa mutanen dake kusa da kofa cikin tashin hankali, inda suka hanzarta fidda shi waje.

An ajiye shi a wajen jami'an tsaron, yayin da mutanen da lamarin ya rudar dasu suka yi kokarin ganin ya farfado ta hanyar kwara masa ruwa tare da amfani da fankar hannu don samar masa iska.

Daga bisani, mutumin ya dawo cikin hayyacinsa, inda aka sanya shi ya zauna don dawo da karfinsa kafin ya bar wurin.

2023: Namadi Sambo, Sule Lamido da wasu jiga-jigan PDP a arewa sun ziyarci Atiku Abubakar

A wani labari na daban, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar, ya gana da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar daga yankin arewa a ranar Talata, 31 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

2023: Jam'iyyar SDP Ta Tsayar Da Gogaggen Sanata Takarar Shugaban Kasa

Daga cikin wadanda suka ziyarci Atiku akwai tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa, tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido.

Hakazalika, abokin hamayyarsa wajen fafutukar tikitin jam’iyyar a zaben fidda dan takarar shugaban kasa na 2023, Mohammed Hayatu-Deen na cikin tawagar da suka ziyarce shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng