Wani Magidanci ya halaka wani mutumi kan kuɗin gutsuren Burodi N100

Wani Magidanci ya halaka wani mutumi kan kuɗin gutsuren Burodi N100

  • Kotu ta umarci a cigaba da tsare wani mutumi, Alhaji Haruna Adu, bisa zargin kashe wani mai Burodi kan kudi N100 a Kwara
  • Jami'in hukumar yan sanda mai gabatar da ƙara, Innocent Owoola, ya shaidawa Kotun Majirtire da ke zamanta Ilorin duk abin da ya faru
  • Alkalin Kotun mai shari'a Abdulganiyu Ajia, bayan jin haka ya ɗage zaman har zuwa ranar 26 ga watan Yuni, 2022

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Kwara - Wata Kotun Majistire da ke zamanta a Ilorin, babban birnin jahar Kwara, ta ba da umarnin a tsare wani magidanci mai suna Alhaji Haruna Adu.

Daily Trust ta ruwaito cewa Kotun ta yi wannan umarni ne bisa zargin mutumin da yin ajalin wani mai sana'ar sayar da Burodi kan kuɗin Burodi N100.

Bajen hukumar yan sanda.
Wani Magidanci ya halaka wani mutumi kan kuɗin gutsuren Burodi N100 Hoto: dailytrust.com
Asali: Twitter

Jami'in hukumar yan sanda mai gabatar da ƙara, Insufekta Innocent Owoola, ya shaida wa Kotun yadda Alhaji Haruna ya dinga sara wa mutumin adda har ya ce ga garin ku nan.

Kara karanta wannan

Atiku, Obi, NNPP da wasu abubuwa 5 da Kwankwaso ya yi magana a hirar da aka yi da shi

Da yake wa Kotu bayani, Owoola, ya ce wanda ake zargin ya sayi Burodi na kimanin Naira N100 daga wurin mamacin, hakan ya yi sanadin samun saɓani tsakanin su kan hanyar da za'a biya kuɗin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jami'in hukumar yan sandan ya gaya wa Kotu cewa:

"Wanda ake zargin ya daɓa wa mutumin adda da dama har sai da ya ga ya daina motsi wato ya mutu."

Wane matakin Alkalin Kotun ya ɗauka?

Da yake yanke hukunci, Alkalin Kotun, Mai shari'a Abdulganiyu Ajia, ya ba da umarnin a cigaba da tsare wanda ake zargi, Alhaji Haruna Adu.

Bayan haka kuma alkalin ya ɗage sauraron ƙarar har zuwa ranar 26, ga watan Yuni na shekarar nan 2022 za'a dawo a cigaba da zama kan lamarin.

A wani labarin kuma Kwamitin jam'iyyar APC zai tantance Sanata Okorocha, Lawan da wasu yan takara 9 a yau

Kara karanta wannan

Ban matsu dole sai na zama shugaban ƙasa a 2023 ba, Kwankwaso ya magantu

Kwamitin jam'iyyar APC na tantance yan takarar shugaban ƙasa ya shirya kammala aikinsa a yau Talata.

Ana sa ran kwamitin ƙarƙashin jagorancin John Oyegun zai tat a nce Lawan Okorocha da sauran yan takara 9.

Asali: Legit.ng

Online view pixel