Kwamitin jam'iyyar APC zai tantance Sanata Okorocha, Lawan da wasu yan takara 9

Kwamitin jam'iyyar APC zai tantance Sanata Okorocha, Lawan da wasu yan takara 9

  • Kwamitin jam'iyyar APC na tantance yan takarar shugaban ƙasa ya shirya kammala aikinsa a yau Talata
  • Ana sa ran kwamitin ƙarƙashin jagorancin John Oyegun zai tatance Lawan Okorocha da sauran yan takara 9
  • A ranar Litinin da daddare, APC ta samu nasarar kammala tantance yan takara 12 da suka haɗa da Tinubu, Badaru da sauran su

Abuja - Jam'iyyar APC a yau zata kammala tantance yan takararta na shugaban ƙasa da tantance Sanata Rochas Okorocha, Ahmad Lawan da wasu mutum 9.

Vanguard ta rahoto cewa duk da Okorocha na tsare a hannun hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon ƙasa (EFCC), APC ta tsara tantance shi a yau.

Sai dai babu tabbacin ko hukumar EFCC zata ba shi damar halartar wurin tantancewar ko kwamitin tantancewa karkashin John Oyegun zai masa wani tanadi na musamman.

Kara karanta wannan

Gabanin zaben fidda gwani: Kotu ta ba da belin Okorocha a zargin almundahanar N2.9bn da ke kansa

Tantance yan takarar APC.
Kwamitin jam'iyyar APC zai tantance Sanata Okorocha, Lawan da wasu yan takara 9 Hoto: Leadership/facebook
Asali: Facebook

Daga cikin waɗan da ake sa ran tantance wa yau sune, tsohon kakakin majalisar wakilai, Dimeji Bankole, gwamna Kayode Fayemi na Ekiti, Sanata Godswill Akpabio, mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, da gwamna Yahaya Bello na Kogi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran yan takarar da za'a tantance yau su ne; Mista Tein Jack-Rich, Dakta Ogbonnaya Christopher Onu, gwamna Ben Ayade na Kuros Riba, da kuma Chief Ikeobasi Mokelu.

Yan takara nawa kwamitin APC ya tantance?

A ranar da kwamitin ya fara aikin da jam'iyyar APC ta dora masa, ya tantance yan takarar shugaban ƙasa 12.

Waɗan da aka tantance a ranar Litinin sun haɗa da, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Chukwuemeka Nwajiuba, Gwamna Mohammed Badaru Abubakar, Uju Kennedy Ohanenye, Fasto Tunde Bakare da Sanata Robert Ajayi Borroffice.

Sauran sune; Nicholas Stanley, Gwamna Dave Umahi, Sanata Ken Nnamani, Rotimi Amaechi, Sanata Ibikunle Amosun da kuma Ahmad Sani Yarima.

Kara karanta wannan

Shirin zaben fidda gwani: Tinubu, wasu 11 sun tsallake tantancewar shugabannin APC

A wani labarin kuma Tsohon gwamnan Kano, Sanata Kwankwaso, ya ce bai matsa dolen dole sai ya zama shugaban kasa a 2023 ba

Sanata Rabiu Kwankwaso ya ce shi ba wai ya matsa ta dole sai ya zama shugaban ƙasa a zaɓen 2023 da ke tafe.

Jagoran NNPP na ƙasa ya ce shi da makamantansa da suka shiga jam'iyyar, sun yi haka ne domin ceto yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel