JAMB: Dalilin da yasa muka rike wasu sakamakon jarrabawar UTME

JAMB: Dalilin da yasa muka rike wasu sakamakon jarrabawar UTME

  • Hukumar jarrabawar JAMB ta bayyana dalilan da suka sanya ta rike sakamakon jarrabawar wasu dalibai
  • Mai magana da yawun hukumar, Dr Fabian Benjamin, ne ya bayyana hakan inda ya lissafa dalilan dalla-dalla
  • Daga cikin dalilan da ya bayyana akwai satar amsa, rashin da’a, keta ka’idojin jarrabawar da kuma rashin cike tantancewar cibiyar zana jarrabawar

Abuja - Hukumar shirya jarabawar shiga jami'o'in Najeriya ta JAMB ta bayyana dalilan da yasa ta rike sakamakon wasu daga cikin daliban da suka zana jarrabawar 2022.

Rahotanni sun kawo cewa hukumar JAMB ta saki sakamakon jarrabawar 2022 a ranar Asabar.

A wata hira da jaridar Punch a ranar Litinin, shugaban sashen hulda da jama’a na hukumar ta JAMB, Dr Fabian Benjamin, ya lissafa dalilin da ka iya sanyawa a rike sakamakon jarrabawar wani dalibi.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Tambuwal ya gana da malaman Islama kan batun dalibar da ta zagi Annabi

JAMB: Dalilin da yasa muka rike wasu sakamakon jarrabawar UTME
JAMB: Dalilin da yasa muka rike wasu sakamakon jarrabawar UTME Hoto: Aminiya
Asali: Depositphotos

Daga cikin dalilan da Benjamin ya bayyana akwai satar amsa, nuna rashin da’a, keta ka’idojin jarrabawar da kuma rashin kammala tantance jarrabawar wasu cibiyoyin da hukumar JAMB ta ke cigaba da yi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma bukaci dalibai da su duba sakamakon jarrabawarsu yadda ya kamata.

Benjamin ya ce:

“Mun saki sakamakon jarrabawar wannan rukunin. Akwai abubuwa da dama da ka iya kai ga rike sakamakon jarrabawa. Yana iya kasancewa saboda satar amsar jarrabawa, idan dalibi ya gaza gudanar da kansa yadda ya kamata, saba tsari ko rashin cike ka’idojin cibiyar zana jarrabawar."

Tun da farko, hukumar JAMB a cikin wata sanarwar da ta fitar ta sha alwashin rike sakamakon jarrabawar daliban da aka kama da satar amsar jarrabawa.

Wani bangare na sanarwar ya ce:

“Zuwa yanzu kimanin dalibai miliyan 1.4 ne suka zana jarrabawar a fadin kasar, inda wasu garuruwa da cibiyoyin jarabawar suka cike adadin da aka basu na wannan shekara yayin da za a saki sakamakon jarrabawar da aka riga aka yi ga daliban.”

Kara karanta wannan

Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi

An saki sakamakon jarabawar JAMB a Najeriya

A wani labarin, hukumar shirya jarabawar shiga jami'o'in Najeriya watau JAMB ta sanar da sakin sakamakon jarabawar bana 2022 da dalibai a fadin tarayya suka zana.

Shugaban sashen hulda da jama'a na JAMB, Fabian Benjamin, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Asabar, rahoton TheNation.

Ya bayyanawa dalibai da suka zana jarabawar cewa za su iya duba sakamakonsu a wayoyinsu na tarho.

Asali: Legit.ng

Online view pixel