Karin bayani: Tambuwal ya gana da malaman Islama kan batun dalibar da ta zagi Annabi

Karin bayani: Tambuwal ya gana da malaman Islama kan batun dalibar da ta zagi Annabi

  • Bayan ganawa da shugabannin tsaro da malaman addinin kirista, Tambuwal ya gana da malaman addinin Islama
  • Wannan ganawa na zuwa ne bayan da wasu dalibai suka kashe wata daliba a harabar kwalejin ilimi ta Shehu Shagari a jihar
  • Daliban sun fusata ne da ganin wani sakon murya da ke bayyana lokacin da dalibar ke zagin Annabi SAW

Jihar Sokoto - Rahoton da muke samu daga gidan gwamnatin jihar Sokoto ya bayyana cewa, gwamna Tambuwal ya gana da malamai da jiga-jigan addinin Islama a jihar bayan kashe wata dalibar da ta zagi Annabi Muhammadu SAW.

A jiya Alhamis ne wani bidiyo ya yadu a kafafen sada zumunta da ke nuna lokacin da wasu dalibai suka kashe tare da kone wata daliba a harabar kwalejin ilimi ta Shehu Shagari da ke jihar ta Sokoto.

Kara karanta wannan

Mafi girman laifi ta yi: Farfesa Maqari ya goyi bayan kashe dalibar da ta zagi Annabi

Malaman Sokoto sun zauna kan batun kashe dalibar da ta zagi Annabi
Da dumi-dumi: Tambuwal ya gana da malaman Islama kan batun dalibar da ta zagi Annabi | Hoto: Sokoto State Governor's Office
Asali: Facebook

Sarkin Musulmi ya yi Allah wadai, kana babban limamin Kacolika a jihar, Bishop Kukah shi ma ya bayyana rashin jin dadinsa.

Ana haka gwamnan ya gana da malaman addini jim kadan bayan ganawarsa da malaman addinin kirista da shugabannin tsaro na jihar, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata sanawar da wakilin Legit.ng Hausa ya samo a shafin Facebook fadar gwamnan Sokoto, ta ce:

"Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto, a baya-bayan nan ya gana da jiga-jigan al’ummar Musulmin jihar a fadar gwamnati da ke Sokoto, domin tattaunawa mafita kan kashe Deborah Samuel."

Ya zuwa yanzu dai ba a bayyana sakamakon tattaunawar gwamnan da malaman addini da sauran shugabannin tsaron ba.

Mafi girman laifi ta yi: Farfesa Maqari ya goyi bayan kashe dalibar da ta zagi Annabi

A wani labarin, babban limamin masallacin Abuja, Farfesa Ibrahim Maqari ya bayyana rashin jin dadinsa ga yadda wata daliba ta shararawa Annabin Allah ashariya a wani faifan sauti da ya yadu a yanar gizo.

Kara karanta wannan

Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi

A bangare guda, malamin na addinin Islama ya amince da daukar doka a hannu ba daidai bane, amma ya nuna goyon bayansa ga hakan idan dai janibin manzon Allah aka taba.

A wasu rubuce-rubuce da ya yada a shafinsa na Twitter, malamin ya nuna fushi tare shiga tashin hankali bisa jin yadda aka ci mutuncin zababben Allah Annabi Muhammadu SAW.

Asali: Legit.ng

Online view pixel