Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun harbe mutum 6 har lahira a Kano, sun sace Basarake

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun harbe mutum 6 har lahira a Kano, sun sace Basarake

  • Wasu yan bindiga sun kai hari kauyen Karfi da ke yankin karamar hukumar Takai a kudancin jihar Kano
  • Maharan sun bindige mutum 9 a harin, shida sun rasu yayin da sauran uku ke kwance a Asibiti, sun sace Dagacin ƙauyen
  • Kakakin rundunar yan sanda reshen Kano, Abdullahi Kiyawa, ya ce tuni aka tura jami'ai yankin da nufin kuɓutar da basaraken da kame maharan

Kano - Wasu yan bindiga da ake tsammanin masu garkuwa ne sun halaka mutum Shida a wani ƙauyen ƙaramar hukumar Takai, a jihar Kano, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Takai na yankin kudancin Kano kuma ta na da nisan kilo mita 80 daga cikin kwaryar birnin Kano kuma ta haɗa iyaka da wasu garuruwa a jihar Jigawa.

Yan bindigan sun farmaki ƙauyen Ƙarfi da ke yankin karamar hukumar Takai kuma suka yi awon gaba da magajin garin ɗan kimanin shekara 53, Abdulyahyah Ilo.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan bindiga sun sake kai kazamin hari kan matafiya a hanyar Abuja-Kaduna

Miyagun yan bindiga.
Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun harbe mutum 6 har lahira a Kano, sun sace Basarake Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigan sun shiga kauyen ne a kan Mashina kuma sun biyo ta Dajin Ringim daga jihar Bauchi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Maharan sun kama hanyar fita daga ƙauyen bayan ɗaukar Basaraken lokacin da mutane suka tara Yan Bijilanti da matasa da nufin bin bayan su.

Ganin haka ya sa yan bindigan suka juyo kuma suka buɗe wa tawagar mutanen da suka biyo bayan su wuta, nan take suka harbe mutum Tara.

Daga cikin mutanen da suka harba, an tabbatar da mutum shida sun rasa rayukan su yayin da ragowar uku ke kwance a Asibiti ana kula da lafiyar su.

Wane mataki hukumar yan sanda ta ɗauka?

Da yake tabbatar da faruwar lamarin kakakin rundunar yan sanda reshen Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce sun tura tawagar jami'an yan sanda zuwa kauyen.

Kara karanta wannan

Al’ummar gari sun tsere cikin jeji yayin da yan bindiga suka farmaki garuruwan Neja

Ya kara da cewa jami'an sun tafi yankin na Takai ne da nufin kuɓutar da Basaraken da aka sace da kuma kame maharan baki ɗaya.

Legit.ng Hausa ta zanta da wani ɗan yankin Takai, Ali, ya shaida mana cewa Basaraken da aka sace nutumin kirki ne da mutane ke ganin girmansa saboda dattakon sa.

Ya shaida wa wakilin mu cewa Sarkin ya na taka rawa wajen ɗora mutane kan tafarki mai kyau kuma yana ba da gudummuwa ga Addinin musulunci.

A jawabinsa ya ce:

"Bayan sun ɗauki sarkin, wani mutumi ya fito ana tsammanin ko ɗauki zai kai ko yayi zaton wani abu ne daban, nan take suka harbe shi har Lahira, suka nufi ɓangaren kudu."
"Sun isa wani gari mafi kusa sai mashin ɗin da Sarki ke kai ya faɗi, shi kuma ya gudu yana neman mutane su taimaka masa. Mutane sun yi kokarin cetonsa amma yan bindigan suka buɗe mu su wuta."

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: Yan bindiga sun banka wuta a Kamfanin rarraba wutar lantarki, sun tafka ɓarna

"Yayin haka ne suka harbi mutum Takwas, biyar suka mutu ragowar uku na kwance a Asibiti. Ana ganin kamar da haɗin bakin wasu makusantan Sarki."

A wani labarin na daban kuma Yan bindiga sun banka wuta a Kamfanin rarraba wutar lantarki, sun tafka ɓarna

Wasu yan bindiga sun banka wuta a kamfanin rarraba wutar Lantarki EEDC da ke jihar Anambra, sun ɓarnata muhimman kayayyaki.

Jami'in hulɗa da jama'a na EEDC, Mista Emeka Ezeh, ya ce jami'an kashe wuta ba su kawo ɗauki ba har sai da Kwamishina ya sa baki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel