Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun sake kai hari kan matafiya a hanyar Abuja-Kaduna

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun sake kai hari kan matafiya a hanyar Abuja-Kaduna

  • Yan fashin daji sun sake tare hanyar Kaduna zuwa Abuja, sun sace mutane da yawa da yammacin nan na Talata
  • Lamarin ya faru ne da yamma misalin ƙarfe 4:30 kuma jami'an tsaro sun kawo ɗauki lokacin yan bindigan sun tafi, inji wani shaida
  • Kakakin yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya ce har yanzun be samu tabbaci daga kwamandan yankin ba

Kaduna - Yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da matafiya da dama a kan sananniyar hanyar Kaduna zuwa Abuja ranar Talata.

Wani shaidan gani da iso ya faɗa wa BBC hausa cewa maharan sun aikata ta'asar ne da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin ranar a kauyen Katari da ke kan hanyar.

Wani sashin hanyar Abuja-Kaduna.
Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun sake kai hari kan matafiya a hanyar Abuja-Kaduna Hoto: @bbchausa
Asali: Twitter

Shaidan ya ƙara da cewa yanzu haka akwai motocin matafiya da dama da suke ajiye a kan hanyar zuwa da kuma dawowa daga Kaduna, maharan sun yi gaba da mutanen ciki.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun aike da sakon sunayen kananan hukumomi 9 da zasu kai hari

A cewarsa sai bayan maharan sun gama cin karensu ba babbaka, sannan jami'an tsaro masu yawa suka dira wurin domin kawo ɗauki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daily Trust ta rahoto cewa yan bindigan dajin sun tare babbar hanyar ne a dai-dai kauyukan Kurmin Kare da Katari, ƙaramar hukumar Kachia, jihar Kaduna, inda suka sace matafiya a motocin haya da na gida.

Wata majiya daga Katari ta ce tun da safiyar Talata, maharan suka farmaki garin suka sace mutum 16, da yamma kuma misalin karfe 4:00 da motsi suka toshe hanya.

Ba mu samu rahoto ba har yanzu - Yan sanda

Kakakin yan sandan Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya ce har yanzun bai samu tabbaci ba daga kwamandan da ke aiki a yankin.

Hanyar mai tsawon kusan kilo mita 155 daga Kaduna zuwa Abuja ta jima ta na fuskantar hare-haren yan bindiga, waɗan da ke kashewa tare da sace matafiya.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Iyaye sun fara tururuwar kwashe 'ya'yan su bayan abu ya Fashe da ɗalibai a Kano

A wani labarin kuma Dirama a Kano yayin da tawagar Kwankwaso ta dira gidan Shekarau awanni bayan tafiyar Ganduje

Siyasar Kano ta ƙara rikicewa musamman tsakanin gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Ibrahim Shekarau

Bayan ziyarar Ganduje gidan Shekarau don hana shi komawa NNPP, Kwankwaso ya tura tawaga kafin zuwansa gidan Shekarau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel