Al’ummar gari sun tsere cikin jeji yayin da yan bindiga suka farmaki garuruwan Neja

Al’ummar gari sun tsere cikin jeji yayin da yan bindiga suka farmaki garuruwan Neja

  • Jama'ar garin Minna, babbar birnin jihar Neja sun shiga zullumi bayan yan bindiga sun farmaki wasu garuruwan da ke kewaye da su
  • Yan bindigar dai sun kai hari Mutun-Daya wanda ke sada babbar birnin zuwa Gwada da kuma Gunu, Zumba da Kuta, hedkwatar karamar hukumar Shiroro
  • Mai magana da yawun yan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar hakan a ranar Litinin

Neja - Hankula sun tashi a kewayen garin Minna, babbar birnin jihar Neja sakamakon wani hari da yan bindiga suka kai kan garuruwan da ke yankin a karshen mako.

An tattaro cewa yan bindigar sun farmaki garin Mutun-Daya wanda ke sada babbar birnin zuwa Gwada da kuma Gunu, Zumba da Kuta, hedkwatar karamar hukumar Shiroro inda yan gudun hijira da dama suka gudu don samun mafaka.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun shiga jihar Kano, sun kashe mutane sun sace wani Basarake

Da yake zangatawa da jaridar The Cable, Abdul Ahmed, wani mazaunin Minna, ya ce matarsa wacce ta tafi biki ta makale a Nakomi, wani kauye kusa da Gunu, lokacin da lamarin ya afku.

Al’ummar gari sun tsere cikin jeji yayin da yan bindiga suka farmaki garuruwan Neja
Al’ummar gari sun tsere cikin jeji yayin da yan bindiga suka farmaki garuruwan Neja Hoto: channelstv,com
Asali: UGC

A cewarsa, sai da matarsa da sauran mazauna yankin suka tsere cikin jeji a yayin harin wanda ya afku a ranar Lahadi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

“Matata ta je bikin aure a kauyen Nakomi lokacin da harin ya afku. Ta ce mazauna kauyukan da ke kusa sun kira don sanar da su cewa yan bindigar sun bar Gunu kuma sun tunkari Nakomi.
“Dukkaninsu sun bar kauyen kuma sun tsere cikin jeji. Matata bata samu dawowa Minna ba, amma ta ce har yanzu wasu mazauna garin na a jeji.”

Wasiu Abiodun, kakakin yan sandan jihar, ya tabbatar da harin a cikin wata sanarwar a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: 'Yan ta'adda sun bindige jami'an 'yan sanda har 3 a jihar Neja

Abiodun ya ce tawagar tsaro sun yi musayar wuta da maharani, yana mai cewa maharani sun raba kansu gida biyu ne a fadin kananan hukumomi uku.

Sanarwar ta ce:

“A ranar 15/05/2022 da misalin karfe 0700hrs, an samu bayani cewa an hango wasu da ake zaton yan bindiga ne a kauyen Zazagha da Injita na karamar hukumar Munya.
“An gaggauta tura tawagar tsaro zuwa yankin, sannan an gano cewa yan bindigar sun raba kansu zuwa kungiyoyi daban-daban yayin da wasu daga cikin yan bindigar suka koma kauyukan Fuka da Daza a karamar hukumar Munya.
“Tawagar tsaron sun koma wadannan yankunan da yan iskan suke sannan fafata da su tare da dakile harin.
“Daga baya yan iskan sun isar da harinsu zuwa kauyen Gwalo, K/Koro na karamar hukumar Paikoro kuma sun yi nasara tare da kwato dabbobi daga hannun yan bindigar.
“An tura matakan tsaro zuwa kauyen Mutun-Daya, ta Gwada, karamar hukumar Shiroro suna samun labarin cewa an gano wata kungiyar yan bindiga a yankin.

Kara karanta wannan

Iftila'i: An tafka ruwan sama a Damaturu, ya rusa gidaje, ya hallaka mutane 5

“An kuma fafata da yan bindigar an kuma kashe wasu daga cikinsu, yayin da sauran suka tsere zuwa jej da raunukan harbi.

Ya kara da cewar Monday Kuryas, kwamishinan yan sanda a jihar, ya kuma jagoranci wata tawagar tsaro daga Minna zuwa Sarkin-Pawa a karamar hukumar Munya.

Legit Hausa ta tuntubi wani mazaunin Minna mai suna Mallam Abubakar inda ya ce:

"Mun je garin Gawu Babangida da ke karamar hukumar Gurara a ranar Lahadi amma haka muka gaggauta komawa Minna bayan mun samu labarin cewa yan bindiga sun kai hari kauyukan da ke hanyar ciki harda wani kauye da ke kusa da Kafin Koro a karamar hukumar Paikoro.
"Ko a gaban gidanmu da ke Gawu, haka muka ga sojoji birjik a hanyarsu ta zuwa kauyen da yan bindigar suka shiga a daren Asabar, inda aka yi garkuwa da wani dattijo a gonarsa."

Yan bindiga sun sace Ɗan majalisar jiha a yankin mazaɓar Gwamnan Anambra

Kara karanta wannan

An kuma, Bam ya tashi a kusa da sansanin Sojojin Najeriya a babban birnin jihar Arewa

A wani labarin, hukumar yan sanda ta jihar Anambra ta tabbatar da sace, Okechukwu Okoye, ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Aguata 1 a majalisar dokokin jihar Anambra.

Honorabul Okoye, wanda ɗan asalin garin Isoufia ne inda gwamnan Anambra, Farfesa Charles Soludo, ya fito, ya shiga hannun masu garkuwa ne a garin Aguata ranar Lahadi.

Kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Anambra, DSP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN).

Asali: Legit.ng

Online view pixel