Idan kuka zabe ni, zan yi yaki da rashawa kamar yadda Buhari ke yi: Godswill Akpabio

Idan kuka zabe ni, zan yi yaki da rashawa kamar yadda Buhari ke yi: Godswill Akpabio

  • Daya daga cikin ministocin Buhari ya yi alkawarin cigaba daga inda maigidansa ya tsaya wajen yaki da rashawa
  • Akpabio ya shiga jerin ministocin gwamnatin shugaba Buhari dake neman takara kujeran shugaban kasa
  • Akpabio ya ce Shugaba Buhari na yaki da rashawa yadda ya kamata

Abuja - Ministan harkokin yakin Neja Delta, Godswill Akpabio, a ranar Alhamis ya ce zai cigaba da yaki da rashawa kamar yadda Shugaba Muhammadu Buhari ke yi idan aka zabesa a 2023.

Akpabio, ya shiga jerin masu neman kujerarn shugaban kasa karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Jawabi yayin hira a shirin PoliticsToday na ChannelsTV, Ministan ya yabawa yaki da rashawan da gwamnatin Buhari ke yi.

A cewarsa:

"Wajibi ne mu cigaba da yaki da rashawa saboda idan ba haka ba, rashawa za ta kashemu. Zan cigaba daga inda Shugaban kasa ya tsaya."

Kara karanta wannan

'Batanci: Bayan Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Deborah a Sokoto, Osinbajo Ya Yi Magana Da Kakkausar Murya

"Abinda yake yi shine yakin rashawa da talauci. Ba zamu iya yaki da rashawa ba tare da mun yaki talauci ba."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Godswill Akpabio
Idan kuka zabe ni, zan yi yaki da rashawa kamar yadda Buhari ke yi: Godswill Akpabio Hoto: NTA

Akpabio, wanda tsohon gwamnan Akwa Ibom ne kuma tsohon Sanata ya ce abubuwa uku manyan matsalolin kasar nan.

A cewarsa sune, matsalar tsaro, rashin hadin kan yan kasa da kuma tattalin arziki.

Ya ce idan yan Najeriya sun zabesa a zaben 2023, zan magance wadannan matsalolin.

Binciken NDDC: Sai an amayo dukkan kuɗaɗen da aka sace, babu sisin kwabo da za mu ƙyalle, Buhari

A wani labarin kuwa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce babu kwabon da zai yi kuka, bayan kammala binciken kudaden Hukumar Bunkasa Yankin Neja Delta, NDDC, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban kasar ya bayyana hakan a Abuja yayin jawabi ta yanar gizo a taron kaddamarwar samfurin dakunan NDDC a jami’ar Uyo da ke Akwa Ibom.

Kara karanta wannan

Buhari ya yi Allah wadai da kashe ɗalibar da ta zagi Annabi a Sokoto, ya nemi a yi bincike

Buhari ya ce an kammala kididdigar kuma an gano inda ko wanne kwabo ya sake yayin da ko wanne mai laifi zai fuskanci hukunci daidai da abinda ya aikata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng