CBN Ta Ci Wasu Bankunan Najeriya Huɗu Tarar N800m Saboda Hada-Hadar Kuɗin Crypto

CBN Ta Ci Wasu Bankunan Najeriya Huɗu Tarar N800m Saboda Hada-Hadar Kuɗin Crypto

  • Wasu bankunan Najeriya guda hudu sun fuskanci fushin babban bankin Najeriya, CBN, saboda saba dokoki na hada-hadar crypto
  • CBN ta ci bankunan hudu tarar Naira miliyan 800 saboda kin rufe asusun bankunan kwastomomi da ke hada-hadar kudin crypto
  • Babban Bankin na Najeriya ta saka dokar hana hada-hadar crypto din ne kan zargin cewa ana amfani da kudin wurin aikata ta'addanci da wasu laifuka

Babban Bankin Najeriya, CBN, ta ci wasu bankunan kasuwanci hudu tarar Naira miliyan 814.3 saboda kin bin dokokinta na rufe asusun hada-hadar kudin intanet wato crypto.

The Nation ta rahoto cewa an ci bankunan tarar ne saboda kin rufe asusun bankunan wasu da ke kasuwancin crypto.

CBN Ta Ci Wasu Bankunan Najeriya Huɗu Tarar N800m Saboda Hada-Hadar Kuɗin Crypto
CBN Ta Ci Wasu Bankuna Huɗu Tarar N800m Saboda Hada-Hadar Kuɗin Crypto. Hoto: The Nation.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Kamfanonin sadarwa zasu yi rashin kwastamomi milyan 72 da aka toshewa layukan waya

A watan Fabrairun bara, CBN ta umurci bankuna su rufe asusun kwastomominsu da ke hada-hadar crypto.

Babban Bankin na Kasa ta umurci bankunan su gano mutanen da ke hada-hadar crypto a bankunansu sannan su rufe asusunsu nan take, rahoton The Nation.

An ci daya daga cikin bankunan tarar Naira miliyan 200 kan zargin cewa wasu kwastomominsu biyu sun yi hada-hadar crypto. An ci bankin na biyu tarar Naira miliyan 500 saboda kin rufe asusun crypto na wasu kwastomomi, a cewar wani sanarwa daga hukumar hada-hadar kudi.

An kuma ci wata bankin tarar Naira miliyan 100 sannan na hudun an ci ta tarar Naira miliyan 14.3 saboda rashin bin dokar na CBN na rufe asusun crypto.

Duk da cewa bankin da aka ci tarar Naira miliyan 200 ta bi dokar CBN, an yi hada-hadar ba tare da saninta ba.

CBN tana da fasahar gano masu kasuwanci da crypto da ba mu da shi, in ji daya daga cikin bankunan da aka ci tara

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: 'Yaushe Najeriya zata gyaru?' Fustattun Matasa sun mamaye tituna

Wakilin bankin ya ce CBN ta iya gano hada-hadar na crypto ne domin tana amfani da 'na'ura ta musamman' wanda sauran bankuna ba su da ita.

Shugaban bankin ya ce sun bukaci CBN ta taimaka musu da irin fasahar da ta ke amfani da shi.

Ya ce:

"Bisa alamu ba za su dawo da kudin ba, amma a yanzu suna musayar fasaha da mu domin mu samu damar dakile irin kwastomomi masu kasuwancin crypto."

Tunda farko, CBN, ta ce ana amfani da kudin na intanet sosai wurin daukan nauyin ta'addanci da karkatar da kudade saboda sirri da ke tattare da hada-hadar crypto.

Buhari: Na Ji Daɗin Yadda Masu Hannu Da Shuni Suka Gane Cewa Canja Najeriya Ba Aikin Mutum Ɗaya Bane

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya yi farin cikin sanin cewa kusoshin Najeriya sun gane cewa canja kasar nan aikin kowa ne, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Ku hana kira fita daga dukka layukan da babu rijista - Buhari ga kamfanonin sadarwa

Kamar yadda kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya bayyana a wata takarda, Buhari ya yi wannan furucin ne a ranar Lahadi a wata liyafa ta girmama shugabannin kwamitin kasuwanci, siyasa, kafafen watsa labarai da sauran ma’aikata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel