Kamfanonin sadarwa zasu yi rashin kwastamomi milyan 72 da aka toshewa layukan waya

Kamfanonin sadarwa zasu yi rashin kwastamomi milyan 72 da aka toshewa layukan waya

  • An toshe layukan wayan mutane sama da miliyan 72 bayan umurnin gwamnatin Najeriya ya fara aiki a ranar Litinin, 4 ga watan Afrilun 2022
  • Kamfanonin sadarwa sun fara kirga asarar da za su yi ta sanadiyar datse layukan wayan yayin da suke fargabar rasa kudaden shiga
  • Sai dai kuma wata majiya ta tabbatar da cewa layukan da aka datse za su iya amfani da intanet, aika sakonnin waya da kuma amsa kiraye-kirayen waya

Kamfanonin sadarwa a Najeriya sun shiga mawuyacin hali sakamakon datse layukan waya sama da miliyan 72 a kasar a ranar Litinin, 4 ga watan Afrilun 2022.

A cewar wani kwararre a bangaren sadarwa, umurnin da gwamnatin tarayya ta bayar zai fi shafar kamfanonin sadarwar ne domin za su yi asarar biliyoyin naira ta sanadiyar hakan.

Masu amfani da waya miliyan 72 sun koka kan rufe layukansu yayin da kamfanonin sadarwa ke kirga asarar su
Masu amfani da waya miliyan 72 sun koka kan rufe layukansu yayin da kamfanonin sadarwa ke kirga asarar su Hoto: finextra.com
Asali: UGC

Kamfanonin sun dogara ne a kan siyar da katin waya don tattara kudaden shiga kuma wannan umurnin babban kalubale ne kai tsaye ga hanyar tattara kudadensu.

Kara karanta wannan

Harin Abuja-Kaduna: Har yanzu ba a ji duriyar fasinjojin jirgin kasa 146 ba, NRC

Hana kiraye-kirayen waya fita

An hana kiran waya fita daga layukansu da ba a hada da lambobin NIN ba, kamar yadda gwamnatin Najeriya ta yi umurni.

Masu layukan ba su cike yarjejeniyar wa’adin ranar 31 ga watan Maris da ma’aikatar sadarwa da tattalin arzikin zama karkashin Isa Pantami ta diba masu ba.

Wata danarwa daga ma’aikatar ta ce kimanin layukan waya miliyan 125 aka hada da lambobin NIN.

Jaridar Punch ta rahoto cewa masu layukan na iya hada su da lambobin kafin hukumar NIMC ta toshe su gaba daya.

Layukan da aka toshe za su iya amfani da intanet da aika sakonni

A cewar hukumar sadarwa ta kasa, akwai layuka masu aiki kimanin miliyan 197.77 a Najeriya a watan Fabrairun 2022.

Sai dai kuma, datse layukan da aka yi bai shafi aika sakon SMS ba, datar waya da kuma kira masu shigowa, kamar yadda wata majiya a daya daga cikin kamfanonin sadarwar ta tabbatar a wani sakon waya da aka aikewa Legit.ng.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Ku hana kira fita daga dukka layukan da babu rijista - Buhari ga kamfanonin sadarwa

Ku hana kira fita daga dukka layukan da babu rijista - Buhari ga kamfanonin sadarwa

A baya mun ji cewa Gwamnatin tarayya ta umurci kamfanonin sadarwa da su hana duk wani kiraye-kirayen waya fita daga lauyukan da ba a hada da NIN ba daga yau Litinin, 4 ga watan Afrilun 2022.

Layukan da abun ya shafa sune wadanda ba a riga an yiwa rijita tare da hada su da lambar shaidar dan kasa ba wato NIN.

Ikechukwu Adinde, daraktan hulda da jama’a na NCC da Kayode Adegoke, shugaban sashen sadarwa na hukumar NIMC ne suka bayyana hakan a wata sanarwa ta hadin gwiwa a ranar Litinin, rahoton The Cable.

Asali: Legit.ng

Online view pixel