Da Dumi-Dumi: Matasa sun toshe babban titin Legas-Ibadan, sun bukaci a gyara Najeriya

Da Dumi-Dumi: Matasa sun toshe babban titin Legas-Ibadan, sun bukaci a gyara Najeriya

  • Wasu fusatattun matasa sun toshe babbar hanyar Legas-Ibadan, sun bukaci yan uwansu su toshe manyan hanyoyin ƙasar nan
  • Matasan sun haɗa babban cunkoso, sun nemi yan siyasa da shugabannin Addinai su faɗa musu menene makomar Najeriya
  • Yanzu haka dai jami'an hukumar yan sanda na can suna kokarin kwantar da lamarin da korar matasan daga kan hanya

Ibadan - Wasu matasa sun toshe babbar hanyar Legas zuwa Ibadan, sun fara ƙone-kone a kowane gefen babban titin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto.

Matasan sun mamaye titin ɗauke da sanduna da kuma allunan rubutu da kuma Bana suna zanga-zangar nuna fushi kan halin da ƙasa ta tsinci kanta a ciki.

Zanga-Zanga a kan titin Legas-Ibadan.
Da Dumi-Dumi: Matasa sun toshe babban titin Legas-Ibadan, sun bukaci a gyara Najeriya Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Banar da suke ɗauke da ita an rubuta kamar haka: "Tambayoyi ga yan siyasa da kuma shugabannin Addinai, menene goben Najeriya?"

Kara karanta wannan

Hotunan 'dan Tinubu yana zantawa da Dangote, Osinbajo da Obasanjo a bazden mahaifiyar Otedola

Kazalika matasan sun rubuta a jikin banar cewa, "Ya kamata a doɗe dukkan manyan hanyoyin dake cikim Najeriya, ba sauran tafiye-tafiye."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wane mataki hukumomi suka ɗauƙa dom shawo kan lamarin?

Yayin da wakilin jaridar ya bi ta hanyar da misalin ƙarfe 3:30 na tsakar ranar Litinin, idonsa ya gane masa yadda jami'an yan sanda ke kokarin kwantar da zanga-zangar.

Kazalika yan sandan ba su yi ƙasa a guiwa ba wajen kokarin ganin matasan sun maida wuƙar su kube sun bar kan hanya.

Lamarin dai ya yi sanadin haɗa cunkoso a kowane hannu na kan babbar hanyar da sauran ƙananan hanyoyi da suka haɗu da babban titin.

A wani labarin kuma Gwamnan Adamawa ya ce Atiku Abubakar ne zai iya kare martabar PDP a babban zaɓen 2023, ya yi mubaya'a

Gwamnan jihar Adamawa, Ahamdu Umaru Fintiru, ya ce Atiku ne zai karbi tutar PDP ta takarar kujerar shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Wata mata ta bayyana shiga takarar shugaban ƙasa a 2023, tace Allah ya faɗa mata zata gaji Buhari

Gwamnan ya bayyana cewa Atiku ne ya dace ya jagoranci Najeriya kuma ya kammala duk wani shirin nasara a zaben fidda gwani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel