Sheikh Nuru Khalid: Idan Zunubi Ne Cewa a Samar Da Tsaro a Najeriya, Na Shirya Shiga Wuta

Sheikh Nuru Khalid: Idan Zunubi Ne Cewa a Samar Da Tsaro a Najeriya, Na Shirya Shiga Wuta

  • Sheikhu Nuru Khalid, Tsohon limamin masallacin Apo Legislative Quarters Central Mosque a Abuja ya kare hudubar da ya yi wadda ta janyo aka tube shi daga limanci
  • A cewar malamin Idan zunubi ne a nemi a samar da tsaro a Najeriya, ya shirya ya shiga wuta saboda hakan ballantana ma ya san ba zunubi bane
  • Sheikh Khalid ya yi wannan karin hasken ne yayin hirar da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels inda ya ce abin da ya ke bukata kawai shine gwamnati ta samar da tsaro

Sheikh Nuru Khalid, wanda ya kafa gidauniyar Islamic Research and Da’awah Foundation ya kare hudubar da ya yi wanda ya janyo aka tube shi daga limanci a masallacin Apo Legislative Quarters Central Mosque a Abuja.

Kara karanta wannan

Sama bai rikito ba a lokacin da na caccaki Jonathan, inji Sheikh Nuru Khalid

Daily Trust ta rahoto yadda aka dakatar da Sheikh din sannan daga bisani aka kore shi baki daya don hudubar da ya yi game da rashin tsaro.

Malamin ya bada wasu shawarwari ga masu zabe da ya ce a dauka idan an gaza samar da tsaro.

Sheikh Khalid: Idan Zunubi Ne Cewa a Samar Da Tsaro a Najeriya, Na Shirya Shiga Wuta
Idan Zunubi Ne Cewa a Samar Da Tsaro a Najeriya, Na Shirya Shiga Wuta, Sheikh Nuru Khalid. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Tun lokacin da mutane da dama a dandalin sada zumunta sun rika tattaunawa game da abin da ya faru da malamin.

A hirar da ya yi da Channels, ya ce ba wani babban abu bane idan an bukaci gwamnati ta samar da tsaro a Najeriya.

Ya furta cewa abin da ya fada kawai shine Shugaban Kasa ya kara kaimi kan abin da ya ke yi a yanzu game da matsalar tsaro, ya jadada cewa harin da aka kai wa jirgin kasa abin bakin ciki ne.

Kara karanta wannan

Duk da shi ma ya na sukar Gwamnati, Ahmad Gumi ya soki hudubar Sheikh Nuru Khalid

Ya ce, "Abin da na yi ba laifi bane, ba laifi bane don na ce abin da ya faru da yan Najeriya a jirgin kasan abin bakin ciki ne.
"Abin bakin ciki ne kuma na ce ya kamata Shugaban kasa ya zage damtse ya kara a kan abin da ya yi. Kuma abin da na ce game da zabe, da kidaya kuri'u, za mu yi magana da su a harshen da suke fahimta kuma mu basu sharadi na cewa su samar da tsaro a Najeriya kafin 2023 ko kuma ba za mu zabe su ba.
"Abin da muka tambaya shine tsaro. Idan zunubi ne a nemi a samar da tsaro a Najeriya. A shirye na ke in shiga wuta saboda hakan. Amma na san ba zunubi bane a bukaci a samar da tsaro a Najeriya."

Ka Jure, Gaskiya Za Ta Yi Halinta: Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Shawarci Sheikh Nuru Khalid

Kara karanta wannan

Korarren Limamin Abuja ya magantu, ya sanar da sabon mukamin da ya samu

A bangare guda, Ɗan takarar shugabancin kasa Farfesa Christopher Imumolen, ya soki dakatarwa da korar babban limamin masallacin Apo Legislative Quarters a Abuja, Shiekh Muhammad Nuru Khalid, Daily Trust ta rahoto.

Kwamitin masallacin ta fara dakatar da malamin ne sannan daga bisani ta more shi gaba daya saboda sukar gwamnatin tarayya kan rashin tsaro da kashe-kashe da aka yi a kasar.

Imumolen, cikin sanarwar da ya fitar ya bukaci malamin da aka dakatar ya zama mai juriya.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel