Ka Jure, Gaskiya Za Ta Yi Halinta: Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Shawarci Sheikh Nuru Khalid

Ka Jure, Gaskiya Za Ta Yi Halinta: Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Shawarci Sheikh Nuru Khalid

  • Farfesa Christopher Imumolen, dan takarar shugabancin kasa ya nuna rashin jin dadinsa game da dakatar tare da korar da Sheikh Nuru Khalid
  • A cikin sakon da ya fitar, Imumolen ya rarashi Sheikh Khalid yana mai cewa ya cigaba da juriya, kada ya karaya bisa abubuwan da za su biyo baya
  • Kwamitin masallacin Apo Legislative Quarters a Abuja ce ta dakatar tare da korar Sheikh Nuru bisa zarginsa da yin huduba da ka iya tunzura al'umma

Ɗan takarar shugabancin kasa Farfesa Christopher Imumolen, ya soki dakatarwa da korar babban limamin masallacin Apo Legislative Quarters a Abuja, Shiekh Muhammad Nuru Khalid, Daily Trust ta rahoto.

Kwamitin masallacin ta fara dakatar da malamin ne sannan daga bisani ta more shi gaba daya saboda sukar gwamnatin tarayya kan rashin tsaro da kashe-kashe da aka yi a kasar.

Kara karanta wannan

Nasan za a rina: Limamin masallacin UniAbuja ya yi martani kan dakatar Sheikh Nuru Khalid

Ka Jure, Gaskiya Za Ta Yi Halinta: Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Shawarci Sheikh Nuru Khalid
Kada Ka Karaya, Gaskiya Za Ta Yi Halinta: Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Shawarci Sheikh Nuru Khalid. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Imumolen, cikin sanarwar da ya fitar ya bukaci malamin da aka dakatar ya zama mai juriya.

Ya ce dakatarwa da aka yi wa Khalid na zuwa ne bayan muhimman taron da suka yi a Abuja.

Akwai alamun masu iko a kasar ba su son a yi magana kan rashin tsaro, Farfesa Imumolen

A cewarsa, akwai alamu ƙarara cewa masu iko a kasar ba su son a riƙa magana kan halin rashin tsaro da ya yi wa kasar katutu.

Ya bukaci malamin ya jure domin za a kai masa hare-hare, musamman wadanda za su rika fake wa da sunan gwamnati.

Imumolen ya tabbatar wa malamin cewa duk inda aka je aka dawo gaskiya za ta yi halinta daga ƙarshe.

Allah Ne Kaɗai Ke Bada Mulki, Kuma Ya Karɓa: Martanin Sheikh Nuru Khalid Bayan Dakatar Da Shi Daga Limanci

Kara karanta wannan

Babu hankali a lamarin: Martanin Shehu Sani da wasu 'yan Najeriya kan dakatar da Sheikh Nuru Khalid

Tunda farko, Babban limanin masallacin Apo Legislative Quarters Mosque, Shiekh Nuru Khalid, wanda aka dakatar kan wa'azin da ya yi da ake yi wa kallon na 'sukar gwamnati' ya yi magana a karon farko, rahoton The Punch.

Khalid, wanda aka fi sani da Digital Imam, a cikin wani sako da ya wallafa cikin harshen larabci ya ce, "Allah ne mafi girma da buwaya. Shi ya ke bada mulki kuma ya karba daga hannun duk wanda ya ga dama lokacin da ya ga dama."

Wannan sakon ya yi kamanceceniya da sakon da ke cikin wasikar da Sanusi Lamido II ya rubuta lokacin da aka tube shi a matsayin sarkin Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel