Sama bai rikito ba a lokacin da na caccaki Jonathan, inji Sheikh Nuru Khalid

Sama bai rikito ba a lokacin da na caccaki Jonathan, inji Sheikh Nuru Khalid

  • Sheikh Nuru Khalid ya ce bai yi danasani maganganun da ya yi wanda ya kai ga sauke shi daga limancin masallacin Juma'a ta Apo da ke Abuja ba
  • Shehin malamin ya ce ba sabon abu bane a wajensa caccakar gwamnati a bangaren da ta gaza
  • Ya ce sama da kasa basu hade ba a lokacin da ya caccaki gwamnatin tsohon shugaba Goodluck Jonathan saboda rashin tsaro

Dakataccen limamin masallacin Juma’a ta Apo da ke Abuja, Sheikh Nuru Khalid, ya ce sukar da yake yiwa gwamnati kan gazawarta ba sabon abu ba ne.

Malamin wanda kwamitin masallacin ya sauke bayan ya soki gwamnatin Buhari, ya ce sama bai rikito ba a lokacin da ya yi Allah-wadai da rashin tsaro a karkashin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Kara karanta wannan

Za a Iya Kawo Karshen 'Yan Ta'adda Cikin Watanni 6, Shugabannin Tsaro Masu Murabus

Daily Trust ta rahoto cewa malamin ya bayyana hakan ne yayin da ya bayyana a shirin gidan talbijin din Trust TV na ‘Daily Politics’.

Sama bai rikito ba a lokacin da na caccaki Jonathan, inji Sheikh Nuru Khalid
Sama bai rikito ba a lokacin da na caccaki Jonathan, inji Sheikh Nuru Khalid Hoto: newsdigest.ng
Asali: UGC

Legit Hausa ta rahoto cewa an dakatar da malamin ne saboda hudubar da ya yi kan matsalar rashin tsaro da kashe-kashe a kasar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan kwamitin ya sallame shi, shehin malamin wanda aka fi sani da ‘Digital Imam’ a shafukan soshiyal midiya ya ce ba’a bashi damar jin ta bakinsa ba.

Ya kuma bayyana cewa Allah ne kadai ke nada mutum da sauke shi daga matsayi.

Kan haka ne, kwamitin masallacin yace ya kore shi gaba daya daga limancin masallacin, cewa bai nuna nadama ba bayan dakatar da shi.

Daily Trust ta kuma rahoto cewa da yake magana a shirin wanda ke kan gudana a yanzu haka, limamin ya ce bai yi danasani kan abubuwan da ya furta ba.

Kara karanta wannan

Wajibi ne APC ta lashe zabe a 2023 saboda ban taba rashin nasara ba, Abdullahi Adamu

Babu hankali a lamarin: Martanin Shehu Sani da wasu 'yan Najeriya kan dakatar da Sheikh Nuru Khalid

A wani labarin, an caccaki kwamitin masallacin Abuja bayan dakatar da limamin masallacin Juma'a na Apo Sheikh Nuru Khalid sakamakon caccakar bangarori daban-daban na gwamnati.

Daya daga cikin wadanda suka yi Allah-wadai da matakin dakatar da malamin dai shi ne tsohon dan majalisar dattawa daga Kaduna ta tsakiya kuma mai fafutukar siyasa da zamantakewa, Shehu Sani.

Sani ya bi sahun ‘yan Najeriya da dama don bayyana ra’ayinsa a shafin Twitter. Ya bayyana dakatarwar a matsayin rashin hankali tsagwaronsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel