Duk da shi ma ya na sukar Gwamnati, Ahmad Gumi ya soki hudubar Sheikh Nuru Khalid

Duk da shi ma ya na sukar Gwamnati, Ahmad Gumi ya soki hudubar Sheikh Nuru Khalid

  • Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi magana a game da abin da ya faru da Sheikh Nuru Khalid
  • Sheikh Nuru Khalid ya yi huduba inda ya yi tir da gwamnatin Najeriya a kan sha’anin rashin tsaro
  • Amma Ahmad Gumi yana ganin bai dace Limamin ya ce mutane za su fasa kada kuri’arsu a zabe ba

Kaduna - Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya tofa albarkacin bakinsa game da abin da ya faru na sauke Shiekh Nuru Khalid daga limanci a garin Abuja.

Kamar yadda labari ya zo mana, babban malami, Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi magana da jaridar Daily Post a ranar Litinin, 4 ga watan Afrilu 2022.

A ra’ayin Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, Nuru Khalid ya yi kuskure a hudubar da ya yi, ya na mai cewa jama’a za su ki kada kuri’arsu a filin zabe.

Kara karanta wannan

Korarren Limamin Abuja ya magantu, ya sanar da sabon mukamin da ya samu

Ahmad Gumi yana ganin fadin wannan magana har ya fi garkuwa da mutanen da ake yi hadari.

Limamin na masallacin Apo ya yi tir da gwamnatin tarayya. Amma malamin addinin yana ganin bai dace Khalid ya furta wadannan kalamai a mimbari ba.

Me ya kamata ayi?

Malamin mai zama a garin Kaduna ya na ganin abin da ya fi dacewa shi ne jama’a su fito su kada kuri’a a wajen zabe domin yin waje da gwamnatin da ta gaza.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ahmad Gumi da Sheikh Nuru Khalid
Sheikh Nuru Khalid da Dr Ahmad Gumi Hoto: BBC/Legit
Asali: UGC

Kira da cewa mutane ba za su yi zabe saboda an gagara tsare rayukansu ba tunanin kirki ba ne a wajen Dr. Gumi, ya na ganin fitinar hakan ta fi satar Bayin Allah.

Dr. Gumi ya na ganin limamin da aka dakatar (daga baya aka sallama gaba daya) ya saki layi.

Babu lissafi a nan - Gumi

Kara karanta wannan

Ka Jure, Gaskiya Za Ta Yi Halinta: Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Shawarci Sheikh Nuru Khalid

“Ra’ayi ne ya sha gaban tunani a nan. Kiran talakawa ka da su ki yi waje da gwamnatin da ta gaza a wajen zabe ya fi garkuwa da mutane muni.”
“Wannan rashin lissafi ne.” - Dr. Ahmed Abubakar Gumi

A baya an saba jin Dr. Gumi ya na zargin gwamnatin da Muhammadu Buhari da gaza tsare rayuka da dukiyoyin al’umma kamar dai yadda ya tuhumi gwamnatin baya.

Jaridar nan ta Daily Post ta ce mutane sun soki wannan matsaya da fakihin malamin ya dauka.

Hudubar Juma'a ta jawo an kori Liman

Ku na da labari cewa Sheikh Nuru Khalid ya rasa kujerarsa ne saboda wata huduba da ya gabatar a kan halin rashin tsaro ganin yadda aka tare jirgin kasa kwanaki.

Kwamitin da ke kula da masallacin a karkashin jagorancin Sanata Sa’idu Dansadau ta dakatar da shi. Daga bisani kuma sai aka ji cewa an kore shi daga aiki gaba daya.

Kara karanta wannan

Nasan za a rina: Limamin masallacin UniAbuja ya yi martani kan dakatar Sheikh Nuru Khalid

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel