Diraktan bankin BOA da aka sace a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna ya samu yanci

Diraktan bankin BOA da aka sace a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna ya samu yanci

  • Yan bindiga sun saki mutum daya cikin dimbin wadanda suka sace a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna
  • Jim kadan kafin su sake shi, yan bindigan sun saki wani faifan bidiyo inda yan bindigan suka yi jawabi
  • Hukumar NRC ta bayyana cewa kawo yanzu an gano mutum 170 cikin fasinjojin da yan bindiga suka kaiwa hari

Kaduna - Sama da mako guda bayan awon gaba da shi da yan bindiga sukayi a jirgin kasan Abuja-Kaduna, diraktan bankin noma, Alwan Ali-Hassan, a ranar Laraba, ya samu yanci.

Bayan harin jirgin da akalla mutane takwas suka rasa rayukansu, iyalan Ali-Hassan suka ce basu ga mahaifinsu ba.

Mai baiwa shugaban kasa shawara da tallafi na musamman, Ismai'l Ahmad, ya tabbatar da hakan a shafinsa na Facebook.

Yace:

"An saki Baba Alwan. Muna addu'a da kokarin ganin an saki sauran. Allah ya kiyaye mu baki daya."

Kara karanta wannan

Wadanda suka kai hari jirgin Abuja-Kaduna sun saki bidiyo, sun ce ba kudi suke bukata ba

Diraktan bankin BOA
Diraktan bankin BOA da aka sace a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna ya samu yanci Hoto: Alwan Hassan
Asali: UGC

Wata majiya ta kusa da iyalan diraktan ta bayyana cewa an sakeshi ne bayan biyan kudin fansa.

Hakazalika wani jami'in bankin ya bayyana cewa Alwan Hassan na Kaduna yanzu bayan samun yanci.

A bidiyon da yan bindigan suka saki, sun bayyana cewa sun saki Alwan Hassan ne bisa yawan shekarunsa kuma albarkacin watar Ramadana.

Har yanzu bamu san inda mutum 21 suke ba, amma muna gyara jiragen: NRC

Hukumar jiragen kasan Najeriya NRC ta bayyana cewa kawo yanzu an gano fasinjojin jirgin kasan da yan bindiga suka sanyawa Bam ranar Litnin guda 170 kuma suna tare da iyalansu.

NRC ta bayyana hakan a jawabin da ta saki ranar Juma'a.

Hukumar tace har yanzu dai akwai sauran mutum 21 da ba'a san inda suke ko halin da suke ciki ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel