Harin jirgin kasan Abj-Kd: Har yanzu bamu san inda mutum 21 suke ba, amma muna gyara jiragen: NRC

Harin jirgin kasan Abj-Kd: Har yanzu bamu san inda mutum 21 suke ba, amma muna gyara jiragen: NRC

  • Hukumar NRC ta bayyana cewa kawo yanzu an gano mutum 170 cikin fasinjojin da yan bindiga suka kaiwa hari
  • Shugaban hukumar yace kawo yanzu sun gyara tarago hudu na jiragen kuma zasu cigaba da gashi
  • Nan ba da dadewa ba, jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna da aka dakatar zai cigaba da jigilar fasinjoji

Legas - Hukumar jiragen kasan Najeriya NRC ta bayyana cewa kawo yanzu an gano fasinjojin jirgin kasan da yan bindiga suka sanyawa Bam ranar Litnin guda 170 kuma suna tare da iyalansu.

NRC ta bayyana hakan a jawabin da ta saki ranar Juma'a.

Hukumar tace har yanzu dai akwai sauran mutum 21 da ba'a san inda suke ko halin da suke ciki ba.

Kara karanta wannan

Harin Abuja-Kaduna: Har yanzu ba a ji duriyar fasinjojin jirgin kasa 146 ba, NRC

Jirgin kasan Abj-Kd
Harin jirgin kasan Abj-Kd: Har yanzu bamu san inda mutum 21 suke ba, amma mun gyara jiragen: NRC Hoto: Official_NRC
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A jawabin da shugaban hukumar NRC, Fidet Okhiria, ya rattafa hannu, yace:

"Hukumar ta yi kokarin tabbatar da lafiyar mutum 170 cikin fasinjojin, yayinda iyalan mutum 21 har yanzu basu san inda suke ba. Hukumar bisa umurnin shugaban kasa na iyakan kokarinta wajen ceto wadanda suka rage."
"Ina farin cikin sanar da ku cewa kawo ranar 1 ga Afrilu 2022, an gyara taragon SP00004, SP00009, SP00012, SP00013 kuma na mayar da su tashar Rigasa. Ranar 2 ga Afrilu, 2022 za'a cigaba da gyaran don jirgin ya cigaba da aiki

Yadda NRC ta yi watsi da gargadin da aka yi mata kan shirin kai harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna

Hukumar kula da ayyukan jirgin kasan Kaduna sun yi karin haske kan gazawar jami’ai a matakai daban-daban wajen dakile farmakin da aka kai wa jirgin kasa, wanda aka samu gargadi tun watanni da suka gabata.

Kara karanta wannan

Yadda NRC ta yi watsi da gargadin da aka yi mata kan shirin kai harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna

Wasikun da aka aike wa hukumomin tsaro da Daily Trust ta gani sun bayyana yadda aka bankado wannan makarkashiyar biyo bayan kutsen da jami’an leken asiri suka yi wanda ya kai ga fitar da sanarwar ga hukumomi daban-daban.

Manyan jami’an tsaro na zargin jami’an hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta Najeriya NRC da kin bin shawarar da aka ba su na takaita zirga-zirgar jiragen kasa zuwa rana kadai banda dare.

Bayanai na baya-bayan nan sun tabbatar da labarin da jaridar Daily Trust ta buga a ranar Alhamis din da ta gabata, wanda ke bayyana cewa harin bam din da aka kai wa jirgin fasinjojin hari da shi duk an san da za a saka shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel