Wadanda suka kai hari jirgin Abuja-Kaduna sun saki bidiyo, sun ce ba kudi suke bukata ba

Wadanda suka kai hari jirgin Abuja-Kaduna sun saki bidiyo, sun ce ba kudi suke bukata ba

  • Yan bindigan da suka sace dimbin matafiya a jirgin kasan Abuja-Kaduna sun bayyana kawunansu a sabon bidiyo
  • Sun ce ba kudi suke bukata ba, gwamnatin tarayya ta san abinda suke bukata kuma ayi gaggawar amsa musu
  • Sun yi kira ga gwamnati ta biya musu bukatunsu idan ba haka ba zasu kashe wadanda ke hannunsu

Yan ta'addan da suka kai hari jirgin kasan Abuja-Kaduna sama da mako daya sun saki bidiyonsu na farko tun bayan harin da yayi sanadiyar halakar mutum akalla takwas.

A sabon bidiyon da suka saki ranar Laraba, sun bayyana cewa ba kudi suke bukata ba, gwamnati ta san abinda suke bukata.

Sun haska bidiyon ne tare da Shugaban bankin noma, Alwan Hassan, inda suka ce zasu sake shi albarkacin tsufarsa da watar Ramadan.

Yan bindiga
Wadanda suka kai hari jirgin Abuja-Kaduna sun saki bidiyo, sun ce ba kudi suke bukata ba Hoto: Daily Nigerian
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga za su ‘kashe’ fasinjojin jirgin kasa, idan Gwamnati ta gaza biya masu bukata

A bidiyon, mutum biyu cikin yan bindigan sun yi magana inda suka ce idan gwamnati bata basu abinda suke so ba zasu hallaka mutanen.

Daya daga cikinsu yace kashe wadanda ke hannunsu ba komai bane.

Kalli bidiyon:

Diraktan bankin BOA da aka sace a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna ya samu yanci

Sama da mako guda bayan awon gaba da shi da yan bindiga sukayi a jirgin kasan Abuja-Kaduna, diraktan bankin noma, Alwan Ali-Hassan, a ranar Laraba, ya samu yanci.

Bayan harin jirgin da akalla mutane takwas suka rasa rayukansu, iyalan Ali-Hassan suka ce basu ga mahaifinsu ba.

A bidiyon da yan bindigan suka saki, sun bayyana cewa sun saki Alwan Hassan ne bisa yawan shekarunsa kuma albarkacin watar Ramadana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel