Bayan shekaru 88, za a yi sallar Taraweehi a Masallacin Hagia Sophia da ke Turkiyya

Bayan shekaru 88, za a yi sallar Taraweehi a Masallacin Hagia Sophia da ke Turkiyya

  • Bayan kwashe shekaru 88 a matsayin gidan tarihi, Hagia Sophia ya cigaba da amsa sunanshi masallaci, sannan ana shirya gabatar da sallar tarawihi ta farko a wannan Ramadana
  • Babban masallacin Turkiyya da aka gina a 532 CE, ya shiga jerin daɗaɗɗun abubuwa a duniya a shekarar 1985, bayan kwashe shekaru 916 a matsayin majami'a
  • Daga bisani ya cigaba da aiki a matsayin masallaci na tsawon shekaru 500 har zuwa 1934 da aka maida shi gidan tarihi

Turkiyya - An samu labari mai daɗi daga babban masallacin Hagia Sophia na Turkiyya, wanda ya sake dawo da sunanshi a matsayin masallaci bayan shekaru biyu da suka wuce.

Kamar yadda Hukumar Anadolu ta ruwaito, babban masallacin Hagia Sophia yana shirya fara tarawihinshi na farko a wannan Ramadanan, bayan kwashe shekaru 88 a matsayin gidan tarihi, The Islamic Information ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Nasan za a rina: Limamin masallacin UniAbuja ya yi martani kan dakatar Sheikh Nuru Khalid

Bayan shekaru 88, za a yi sallar Taraweehi a Masallacin Hagia Sophia da ke Turkiyya
Bayan shekaru 88, za a yi sallar Taraweehi a Masallacin Hagia Sophia da ke Turkiyya. Hoto daga theislamicinformation.com
Asali: UGC

Za a yi sallar tarawihi a masallacin Hagia Sophia bayan shekaru 88, The Islamic Information ta ruwaito.

Ba sallar tarawihi kaɗai ba, an samu labarin yadda aka shirya gudanar da abubuwa da dama na Ramadana a masallacin Hagia Sophia, kuma ana sa ran masu bauta da dama su ziyarci masallacin a watan mai albarka.

Masallacin Hagia Sophia a da yana matsayin gidan tarihi tun 1934.

Duk da a shekarar 2020 ya amsa sunan sa masallaci, sannan an buɗe shi don musulmai su yi bauta a ranar 24 ga watan Julin shekarar.

Sai dai a rashin sa'a, cutar Korona ta fara yaɗuwa a ƙasar Turkiyya a shekarar. Hakan ya tilasta masallatai rufewa don rage hatsarin kamuwa da cutar.

Daga ƙarshe dai, a wannan shekarar, masallacin nan zai cigaba da aiki a matsayin wurin bauta ga musulmai a cikin watan Ramadana; saboda an yi wa mutane da dama riga kafin cutar, yawan masu kamuwa da cutar da yawan waɗanda cutar ke halakawa ya fara raguwa.

Kara karanta wannan

Sifetan dan sanda ya sheka lahira yana tsaka da 'kece raini' da bazawara a otal

Mene ne tarihin Masallacin Hagia Sophia?

An gina masallacin Hagia Sophia a 532 CE, sannan ya dauki tsawon shekaru 916 a matsayin majami'a.

Sai dai, a 1453, an maida Hagia Sophia masallaci bayan Istanbul ta samu ƴancin kanta. Masallacin ya cigaba da aiki har tsawon shekaru 500 zuwa 1934, lokacin da aka mayar da shi gidan tarihi.

UNESCO sun saka Hagia Sophia a jerin abubuwa daɗaɗɗu a duniya a 1985, saboda yadda ya sha bambam da saura, wanda yake wurin bautar addinai guda biyu.

Hagia Sophia na ɗaya daga cikin fitattun masauƙin baƙi a Turkiyya.

A duk shekara, dubu ɗaruruwan mutane na ziyartarshi, waɗanda ke zuwa daga sasannin duniya daban-daban.

An bude sabon Masallaci mafi girma na biyu a yankin Afirka ta yamma a kasar Ghana

A wani labari na daban, bayan tsawon lokaci ana gini, an bude sabon babban Masallacin kasar Ghana wanda ake ikirarin cewa shine mafi girma a yankin Afrika ta yamma.

Kara karanta wannan

Yan Kwamitin Masallaci sun dakatad da Sheikh Nuru Khalid daga Limanci a Abuja

Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo Addo, da kansa ya kaddamar da Masallacin a ranar Juma'a, 16 ga watan Yuli, 2021.

Shugaban kasan ya bayyana cewa akwai katafaren asibiti a cikin Masallacin da kuma dakin karatu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel