Yan Kwamitin Masallaci sun dakatad da Sheikh Nuru Khalid daga Limanci a Abuja

Yan Kwamitin Masallaci sun dakatad da Sheikh Nuru Khalid daga Limanci a Abuja

  • Kan hudubar Juma'a da yayi, kwamtin masallaci ta tsige Limaman Masallacin Apo Legislative Quaters dake Abuja
  • Sheikh Nuru Khalid ya shahara da hudubobi kan yadda lamarin tsaro ya ta'azzara a Najeriya karkashin mulkin shugaba Buhari
  • Kwamitin Masallacin tace hudubarsa ta karshe da yayi ta sabawa koyarwan addinin Musulunci

Abuja - Mambobin Kwamitin jagorancin masallacin rukunin gidajen ƴan majalisu da ke unguwar Apo a birnin tarayya Abuja, sun dakatar da Sheikh Nuru Khalid daga limanci a Masallacin.

Shugaban kwamitin Masallacin Sanata Saidu Muhammed Dansadau a jawabin da ya saki ya bayyana cewa an sallami Malam Nuru Khalid ne bisa hudubar da yayi ranar Juma'a, 2 ga Afrilu, 2022, rahoton BBC Hausa.

Mambobin kwamitin sunce hudubar Malam Nuru Khalid na tunzura jama'a.

A cewar jawabin:

"Ina mai sanar da kai cewa an dakatar da kai daga Limanci a Masallacin ƴan Majalisar da ke shiyyar Apo Abuja daga yau 2/4/22 har zuwa wani lokaci."

Kara karanta wannan

Wata mata ta bayyana shiga takarar shugaban ƙasa a 2023, tace Allah ya faɗa mata zata gaji Buhari

"An ɗauki wannan matakin ne saboda hudubar Juma'a ta tunzurawa a ranar 1/4/22 inda ka ba mutane shawarar kada su yi zaɓe a 2023 har sai 'yan siyasa sun amsa wasu tambayoyi."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ya kamata a ce ka ba su shawara su fito zaɓe don kawar da waɗanda suka saɓa wa Allah, da masu zaɓe da kuma ƙasa."

Yan Kwamitin Masallaci sun dakatad da Sheikh Nuru Khalid daga Limanci a Abuja
Yan Kwamitin Masallaci sun dakatad da Sheikh Nuru Khalid daga Limanci a Abuja
Asali: Twitter

Me Sheikh Nura Khalid ya fadi a hudubar?

A cikin hudubar, malamin ya faɗi matakin da ya kamata talakawa su ɗauka idan har gwamnati ta bari aka ci gaba da kashe su, na kin fitowa zaɓe.

Sheikh Nuru Khalid a huɗubarsa yace:

"Sharadin talakan Najeriya ya zama guda ɗaya kawai, ku hana kashe mu, mu fito zabe, ku bari a kashe mu, ba za mu fito zaɓe ba, tun da ku ba abin da kuka sani sai zabe,"

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel