An bude sabon Masallaci mafi girma na biyu a yankin Afirka ta yamma a kasar Ghana
1 - tsawon mintuna
- An kaddamar da babban Masallacin kasar Ghana
- Masallacin na da siffa irin na Hagia Sophia dake kasar Turkiyya
- Shugaban kasar Ghana ya bude Masallacin
Bayan tsawon lokaci ana gini, an bude sabon babban Masallacin kasar Ghana wanda ake ikirarin cewa shine mafi girma a yankin Afrika ta yamma.
Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo Addo, da kansa ya kaddamar da Masallacin a ranar Juma'a, 16 ga watan Yuli, 2021.
Shugaban kasan ya bayyana cewa akwai katafaren asibiti a cikin Masallacin da kuma dakin karatu.
Hakan ya bayyana a jawabin da ya daura a shafinsa na Facebook da yammacin Juma'a.
Ya kara da cewa Masallacin na dauke da dakin ajiye gawawwaki da wajen ajiyan magunguna.
Yace:
"A ranar Juma'a, 16 ga Yuli, 2021, na kaddamar da Masallacin kasar Ghana don amfanin Musulman kasarmu."
"Wannan Masallaci ne mafi girma a yammacin Afrika, akwai ofishin babban limamin kasar, katafaren asibiti da gidan magani, dakin karatu da kuma dakin ajiye gawawwaki."
Yan Najeriya sun tifa albarkacin bakinsu
Attahiru Ibrahim Yace:
MASHA Allah. Allah kara dauka musulunci
Zaitun Bint Zaid el'Kanawee tace:
Masha Allah,amma ya ginu kuwa sosai
Abdulhakeem Abdullahi yace:
Masha Allah Allah yakara daukaka musulmai da musulunci
Babagana Alhaji Adam yace:
Masha ALLAH, Nayi Farin ciki Sosai Wallahi
يوسف بن ابى بكر yace:
Masha Allah.
Allah yanuna mana an kammala na garin yabo
·
Asali: Legit.ng