Sifetan dan sanda ya sheka lahira yana tsaka da 'kece raini' da bazawara a otal

Sifetan dan sanda ya sheka lahira yana tsaka da 'kece raini' da bazawara a otal

  • Sifetan dan sanda mai shekaru 47 mai suna Michael Ogunlade ya sheka lahira yana tsaka da saduwa da bazawara a otal
  • Ma'aikatan otal din sun sanar da cewa sun biya kudin daki amma jim kadan sai matar ta fito tana ihun ya fadi
  • Jami'an 'yan sanda sun gaggauta tafiya da shi asibiti inda kafin su isa yace ga garinku, matar ta fada jimami don tace sun dade suna tare

Ibadan - An tabbatar da mutuwar wani Sifeta a hukumar ‘yan sandan Najeriya mai suna Michael Ogunlade mai shekaru 47 da haihuwa a sashen Operation Eleyele, yayin da yake lalata da wata masoyiyarsa ta sirri, wacce aka sakaya sunanta, a Otel din The Classical wanda aka fi sani da White House, Oke-Ado a Ibadan.

Wata majiya mai tushe ta shaida cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:15 na yammacin ranar Lahadi, jim kadan bayan da su biyu suka biya kudin dakin otal din, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan sandan Kano sun bindige masu satar mutane 3, sun ceto wasu mutane

Sifetan dan sanda ya sheka lahira yana tsaka da 'kece raini' da bazawara a otal
Sifetan dan sanda ya sheka lahira yana tsaka da 'kece raini' da bazawara a otal. Hoto daga Vanguardngr.com
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar wani shaidan gani da ido, sun hadu da shi a matakala amma kasancewar yana daya daga cikin ma’aikatan, bai iya kallon fuskokinsu ba, don haka sai ya yi banza da su. Bayan 'yan mintoci kaɗan sai matar ta fito da gudu ta fara kuka tana cewa mutumin ya fadi.

“Mun yi gaggawar sanar da ‘yan sandan da ke ofishin ‘yan sanda na Iyaganku, inda suka zo da gaggawa amma kafin su kai shi wani asibiti da ke kusa, ya ce ga garinku.” Ta furta.

Vanguard ta ruwaito cewa, rahotanni masu cin karo da juna sun ce ya mutu ne sakamakon aike tsaw wani mutum ya yi wa matar, yayin da wasu suka ce marigayin ya yi amfani da abin kara kuzari wajen saduwa da ita.

Daya daga cikin ma’aikatan otal din da ta so a sakaya sunanta ta ce: “Ban santa ba, amma yadda take magana bayan faruwar lamarin, ta yi rashin mijinta tun 2014. Har ta ce marigayin ne ya dauki nauyin biyan kudin makarantar ‘ya’yanta sama da shekaru biyar da sauran ababen bukata na gida.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Ƴan Bindiga Sun Sace Sifetan Ƴan Sanda Da Wasu Mutane 3 Yayin Da Suke Sallah a Masallaci

“A ina zan fara kuma? Shi ne mai taimakona. Ya kasance kamar mijina domin muna haduwa kowaceranar Lahadi. Ya na yi min duk wani abu da na tambaye shi.” Daya daga cikin ma’aikatan otal din ta ruwaito hakan daga bakin matar bayan faruwar lamarin.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, PPRO, Adewale Osifeso, ya gagara saboda ba a samun lambar wayarsa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel