Cikakken jerin sunayen yan sandan da Sufeta Janar ya sallama daga aiki kan kulla makirci

Cikakken jerin sunayen yan sandan da Sufeta Janar ya sallama daga aiki kan kulla makirci

  • Hukumar yan sandan Najeriya ta kori jami'anta guda Tara bisa zargin kulla makircin shiga yajin aiki a hukumar
  • Wasu alamu a Hedkwatar yan sanda ta ƙasa dake Abuja sun nuna cewa Sifeta Janar na ƙasa, Usman Baba, ya amince da matakin
  • Bayanai sun nuna cewa hukumar ta gano mutanen ne bayan bibiyan tattaunawarsu a wayar salula

Abuja - Hukumar yan sandan ƙasar nan ta sallami Jami'anta guda Tara bisa zargin kulla makircin shiga yajin aiki a hukumar, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Sifeta Janar na ƙasa, IGP Usman Baba, ya amince da matakin sallamar yan sandan a wasu alamu da shugaban yan sandan ya nuna a Hedkwatar Abuja, biyo bayan abin da suka aikata.

Hukumar ta gargaɗi yan sanda a rassanta da kuma tawaga-tawaga da rundunonin yan sanda a faɗin ƙasar nan kan lamarin.

Kara karanta wannan

Abun Kunya: Babban abokin Ango ya sace danƙareriyar kyautar Amarya mai tsada a Kano

Sufetan yan sanda na ƙasa, Usman Baba.
Cikakken jerin sunayen yan sandan da Sufeta Janar ya sallama daga aiki kan kulla makirci Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Jami'an yan sanda sun yi barazanar tsunduma yajin aiki kan ƙin aiwatar da ƙarin Albashi na kashi 20 da majalisar zartarwa ta ƙasa (FEC) ta amince da shi a watan Disamba, 2021.

Bayan rahoton shirin shiga yajin aikin ya watsu, IGP ya gargaɗi jami'ansa su dakatar da kulle-kullen shiga yajin aiki ko kuma su fusakanci fushin hukumar, kamar yadda The Cable ta rahoto.

Sifetan ya yi wannan gargaɗin yayin da yake jawabi ga dakarun yan sanda na hedkwatar Bampai dake jihar Kano, ranar 24 ga watan Maris.

IGP Baba ya kuma tura tawagar manyan yan sanda zuwa wasu rassan ƙasar nan domin su kwantar da hankulan jami'ai tare da alƙawarin za'a bibiyi kadin lamarin ƙarin albashin.

A wata alamar dake nuna tabbacin an sallami yan sandan guda 9, hukumar ta umarci a kwace Kakin su kuma a zare sunayen su daga tsarin biyan Albashi IPPIS tun daga ranar 1 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: 'Yaushe Najeriya zata gyaru?' Fustattun Matasa sun mamaye tituna

Bayanai sun nuna cewa asirin yan sandan ya tonu ne ta hanyar bibiyar tattaunawarsu ta wayar salula har kuma aka cafke su.

Jerin sunayen yan sandan

1. AP/No. 245800 – Insufekta Nanoll Lamak

2. AP/ NP 287568 – Insufekta Amos Nagurah

3. F/No. 271367 – Sajan Onoja Onuche

4. F/No. 442680 – Sajam Franklin Agughalau

5. F/No. 495378 – Sajan Emmanuel Isah

6. F/No. 508168 – Sajan Adesina Ismail

7. F/No. 508282 – Sajan Osoteku Ademola

8. F/No. 525839 – Kwansutabul Ehighamhen Favour Ebele

9. F/No. 528222 – Kwansutabul Ubong Inem

Yayin da aka nemi jin ta bakin muƙaddashin kakakin hukumar yan sanda ta ƙasa, CSP Muyiwa Adejobi, ya yi alƙawarin bincike kafin ya dawo gare mu.

A wani labarin kuma Jerin sharuddan da INEC ta gindaya wa jam'iyyun siyasa, ta shirya fatali da yan takara a zaɓen 2023

Hukumar INEC ta kara tuna wa jam'iyyun siyasa jadawalin sharuɗɗan da ta kafa da abun da ka iya biyo baya a zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jirgin yaƙin Sojojin Najeriya ya halaka dandazon yan bindiga a bodar Kaduna da Neja

INEC ta gargaɗi jam'iyyu a kan bin dukkan tanade-tanaden doka da demokaraɗiyya wajen fitar da yan takara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel