Abun Kunya: Babban Abokin Ango ya sace danƙareriyar kyautar da aka ba Amarya a Kano

Abun Kunya: Babban Abokin Ango ya sace danƙareriyar kyautar da aka ba Amarya a Kano

  • Babban Abokin Ango ya fakaici lokacin da ba su nan, ya shiga har cikin gida ya sace kyautukan da aka ba Amarya
  • Lamarin dai ya faru ne a yankin Gaida dake ƙaramar hukumar Kumbotso ta jihar Kano, wanda ake zargin yace sharrin shaiɗan ne
  • A halin yanzun yan Bijilanti sun yi ram da mutumin, za su miƙa wa yan sanda bayan kammala bincike

Kano - Babban abokin Ango a yankin Gaida dake ƙaramar hukumar Kumbotso, a jihar Kano, ya yi awon gaba da wata danƙareriyar kyauta da aka bai wa Amarya.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa kyautar da abokin Ango ya sace zata kai darajar kuɗi kusan N500,000.

Rahoto ya nuna cewa lamarin ya faru mako ɗaya bayan kammala shagalin bikin, yayin da wanda ake zargin ya samu makullan gidan sabbin ma'auratan.

Kara karanta wannan

Matar Aure mai juna biyu ta daɓa wa mijinta wuƙa har lahira yana tsaka da bacci kan zai ƙara Aure

An kama abokin Ango bisa zargin sata.
Abun Kunya: Babban Abokin Ango ya sace danƙareriyar kyautar da aka ba Amarya a Kano Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Da yake jawabin kan abun da ya faru, kwamandan yan Bijilanti a Gaida, Shekarau Ali, ya bayyana cewa Ango ne da kansa ya kawo rahoto kuma bayan bincike suka cafke wanda ake zargi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, Abokin Angon ya samu makullan gidan daga hannun yan uwan Amarya, tare da alƙawarin cewa zai damƙa wa Ango makullan hannu-da-hannu.

Ya ƙara da cewa:

"Angon ya buƙaci ya kawo masa makullan amma ya ƙi. Lokacin da ya ga ma'auratan sun tafi Anguwa, sai ya buɗe gidan ya shiga, ya ɗauki akwatunan kyauta da kayan abinci."

Kwamandan yan Bijilantin ya bayyana cewa yanzu suna ƙara bincike kan wanda ake zargin kuma ba da jimawa ba zasu miƙa shi hannun yan sanda.

Shin ya amsa laifinsa?

A ɓangarensa, wanda ake zargin ya amsa laifin da ake tuhumarsa, ya ce sheɗan ne ya rinjaye shi har ya ci amanar abokinsa kuma ya nemi gafararsa.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari a ayyana shiga tseren kujerar gwamna a zaɓen 2023, ya yi alƙawarin ba zai ci amana ba

Haka nan kuma ya bayyana cewa ya ba da gudummuwa wajen bikin abokin nasa ya kashe sama da N400,000.

A wani labarin kuma Wata mata ta bayyana shiga takarar shugaban ƙasa a 2023, tace Allah ya faɗa mata zata gaji Buhari

Wata sabuwar yar takarar kujerar shugaban ƙasa a Najeriya ta bayyana ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APGA.

Angela Johnson, ya sanar da cewa Allah ne ya umarce ta da ta fito takara domin ita ce zata gaji shugaba Buhari a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel