Ramadan 2022: Farashin kayan Abinci ya yi tashin gwauron zaɓi a kasuwannin Kwara, mutane sun koka

Ramadan 2022: Farashin kayan Abinci ya yi tashin gwauron zaɓi a kasuwannin Kwara, mutane sun koka

  • Bayan shigowar watan Azumin Ramadan, bincike ya nuna cewa Farashin kayan abinci sun yi tashin gwaurin zabi a jihar Kwara
  • Kayan itatuwa, kayan lambu, shinkafa, Kankana da sauran kayayyakin da aka fi amfani da su a Azumi sun yi tashin wuce tsammani
  • Mutane da ma'aikatan gwamnati waɗan da ke amfani da kayayyakin sun koka duba da halin rashin kuɗi

Kwara - Kwanaki uku kacal da fara Azumin watan Ramadan, Farashin kayayyakin abinci da sauran kayan masarufi ya yi tashin gauron zaɓi a mafi yawan kasuwannin jihar Kwara.

Farashin kayan itace, kayan lambu, kankana, da kayan sha da mutane suka fi bukata a lokacin watan Azumi, sun yi tashin da ba'a yi tsammani ba.

Wasu daga cikin mutanen dake amfani da irin waɗan nan kayayyaki da suka zanta da Daily Trust sun nuna rashin jin daɗin su ƙarara da tashin Farashin duba da halin ƙaƙanikayin tattalin arziƙi da ƙasar nan ke ciki.

Kara karanta wannan

Abun Kunya: Babban abokin Ango ya sace danƙareriyar kyautar Amarya mai tsada a Kano

Farashin kayan masarufi a Kwara.
Ramadan 2022: Farashin kayan Abinci ya yi tashin gwauron zaɓi a kasuwannin Kwara, mutane sun koka Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A kasuwar Obbo, bincike ya bayyana cewa farashin Shinkafa, Wake, Kayan itace, da sauran kayan sha na ruwa sun tashi da kaso 15 cikin ɗari.

Yadda mutane suka ji da lamarin

Wani Kwastoma, Abolore Hussein, wanda ya bayyana cewa zuwansa na farko kenan tun bayan fara Azumin Ramadan, ya nuna fusata da damuwa kan tashin farashin.

A cewar wata Kwastoma mai suna Sidikat Yusuf, "A baya muna siyan kashin Tumaturi N150 amma yanzu ya koma N300. Ƙaramin bokiti da muke siya N700 yanzu ya koma N1,000."

Haka nan kuma Misis Garuba Halimat ta koka kan yadda farashin Kwandon Tumatur ya tashi daga N21,000 zuwa N27,000.

Kazalika wata ma'aikaciyar gwamnati, Hajia Lateefat Abdullahi, ta ce Lita biyar na Man kayan lambu da suke siya N5,160 kafin zuwan Ramadan, yanzun ya koma N8,000.

Kara karanta wannan

Talakawa miliyan biyu za su fara jin alat na Biliyan N20bn duk wata daga Yuni, Gwamnatin Buhari

Ta kuma ƙara da cewa Buhun shinkafa ya koma N32,000 daga N29,000 da ake siyarwa kafin fara Azumi.

"Farsahin man da ake samar wa daga kayan lambu ya yi tashin da ya wuce tunani baki ɗaya."

Bukola Oladimeji, ta ce ta sayi ƙaramar kwallon Kankana wacce ake siyarwa N300 a baya kan Naira N700. Ta ƙara da cewa farashin Katan ɗin madara three crown ya karu da sama da N1,000.

A wani labarin kuma Binciken Mako: Kayan Masarufi uku da suka yi tashin gwaurin zabi a babbar kasuwar Najeriya

Farashin kayayyakin masarufi a kasuwar jihar Legas na sama suna ƙasa saboda kalubalen tsaro, canjin kudi da sauran su.

Karancin Man fetur ba ya cikin abubuwan da suka jawo tashin kayan, sai dai yan kasuwa sun ce rashin dai-daiton tattalin arziki ne babban dalili.

Asali: Legit.ng

Online view pixel