Gwarzon namiji: Matashin da yayi wuff da mata 9 a rana 1 yace yana son karin wasu 2

Gwarzon namiji: Matashin da yayi wuff da mata 9 a rana 1 yace yana son karin wasu 2

  • Arthur O Urso ya karade kanun labarai a shekarar 2021 bayan daurin aurensa da mata 9 a lokaci daya a wani bikin aure da aka gudanar a birnin São Paulo na Brazil
  • Matashin dan kasar Brazil yanzu yana ganin cewa adadin matansa zai ragu zuwa 8 saboda daya daga cikinsu tana son sakinsa
  • Yayin da yake bayyana bakin ciki da mamakin hukuncin da daya daga cikin matansa ta yanke, ya bayyana cewa yana son ya kara auren mata biyu

Brazil - Wani matashi mai suna Arthur O Urso, wanda ya auri mata 9, ya bayyana cewa yana son ya auri wasu mata biyu don kai adadin matansa zuwa 10 tunda daya na son fita.

Mirror.co.uk ta ruwaito cewa, dan asalin kasar Brazil din ya zama abin burgewa a intanet a shekarar 2021 bayan ya bi kanun labarai bayan ya tare da mata 9 a lokaci daya a wani karamin biki da ya gudana a birnin São Paulo na kasar Brazil.

Kara karanta wannan

Sifetan dan sanda ya sheka lahira yana tsaka da 'kece raini' da bazawara a otal

Gwarzon namiji: Matashin da yayi wuff da mata 9 a rana 1 yace yana son karin wasu 2
Gwarzon namiji: Matashin da yayi wuff da mata 9 a rana 1 yace yana son karin wasu 2. Hoto daga Jam Press
Asali: UGC

Daya daga cikin matan Arthur na son sakinsa

Mahaifin yaro dayan da farko yana tare da matarsa ta farko mai suna Luana Kazaki amma daga bisani suka kulla aure da ita yayin da ya auri sauran 8 a lokaci daya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai kuma, daya daga cikin matan mai suna Agatha ta rabu da shi kuma tana bukatar saki saboda tace tana kewar zamanta mace daya a wurin mijinta.

Daily Mail ta ruwaito cewa, Agatha tana son ya rabu da ita ne saboda tana kaunar zama da Arthur ita daya tilo.

A yayin martani ga yunkurin Agatha, Arthur wanda yace yana son haihuwa da kowacce mace daga cikin matansa, ya ce ya yi bakin ciki da mamakin abinda Agatha ke yunkurin yi.

Ya ce:

"Abun babu hankali a ciki, ya zama dole mu yi hakurin zama da juna. Na yi takaicin rabuwa da ni da ta yi amma na sha mamaki da na ji dalilinta.

Kara karanta wannan

Kannywood: An Taɓa Ɗaure Min Hannu Aka Jefa Ni Cikin Rafi Saura Ƙiris Kada Ya Yi Kalace Da Ni, Baba Musa na Kwana Casa'in

"Na san na yi rashin mata, amma babu dadewa zan maye gurbinta da wata."

Abinda mai karatu ya dace ya sani ne cewa an haramta auren mace fiye da daya a kasar Brazil.

Hotunan auren matashin da yayi wuff da tsulan-tsulan 'yammata 2 a rana daya

A wani labari na daban, shugaban matasan jam'iyyar APC na gundumar Garki, Hon Babangida Sadiq Adamu a ranar Asabar da ta gabata ya aura mata biyu a rana daya a Abuja.

Adamu ya auri Malama Maimuna Mahmud da Malama Maryam Muhammad Na'ibi a ranar Asabar, 6 ga watan Maris din 2021.

Daurin auren farko an yi shi ne a masallacin Juma'a na Kada Bmiko kusa da makarantar firamare ta Kado Bmiko, 1st Avenue dake Gwarinpa da karfe 10:00 na safe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel