Hotunan auren matashin da yayi wuff da tsulan-tsulan 'yammata 2 a rana daya

Hotunan auren matashin da yayi wuff da tsulan-tsulan 'yammata 2 a rana daya

- Matashi kuma shugaban matasan jam'iyyar APC a Garki ya aura tsula-tsulan mata biyu a rana daya

- Kamar yadda aka bayyana, an daura auren biyu duk a Abuja a ranar Asabar, 6 ga watan Maris 2021

- Bayan daurin auren, an cigaba da kasaitacciyar liyafa a dakin taro na Apo Resettlement dake Abuja

Shugaban matasan jam'iyyar APC na gundumar Garki, Hon Babangida Sadiq Adamu a ranar Asabar da ta gabata ya aura mata biyu a rana daya a Abuja.

Adamu ya auri Malama Maimuna Mahmud da Malama Maryam Muhammad Na'ibi a ranar Asabar, 6 ga watan Maris din 2021.

Daurin auren farko an yi shi ne a masallacin Juma'a na Kada Bmiko kusa da makarantar firamare ta Kado Bmiko, 1st Avenue dake Gwarinpa da karfe 10:00 na safe.

KU KARANTA: Da duminsa: Gagararren makashin makiyayi, Iskilu Wakili ya shiga hannun hukuma a Oyo

Hotunan auren matashin da yayi wuff da tsulan-tsulan 'yammata 2 a rana daya
Hotunan auren matashin da yayi wuff da tsulan-tsulan 'yammata 2 a rana daya. Hoto daga @Lindaikeji
Source: Twitter

Auren na biyu an daura shi ne a masallacin Juma'a na kauyen Garki, Garki II a Abuja wurin karfe 1:30 na rana.

An yi kasaitacciyar liyafa a babban dakin taro na Apo Resettlement, Abuja. Shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Hotunan auren matashin da yayi wuff da tsulan-tsulan 'yammata 2 a rana daya
Hotunan auren matashin da yayi wuff da tsulan-tsulan 'yammata 2 a rana daya. Hoto daga @Lindaikeji
Source: Twitter

KU KARANTA: Tsohuwar matar Fani-Kayode ta maka shi gaban kotu, tana son karbar 'ya'yansu

Hotunan auren matashin da yayi wuff da tsulan-tsulan 'yammata 2 a rana daya
Hotunan auren matashin da yayi wuff da tsulan-tsulan 'yammata 2 a rana daya. Hoto daga @Lindaikeji
Source: Twitter

Hotunan auren matashin da yayi wuff da tsulan-tsulan 'yammata 2 a rana daya
Hotunan auren matashin da yayi wuff da tsulan-tsulan 'yammata 2 a rana daya. Hoto daga @Lindaikeji
Source: Twitter

A wani labari na daban, tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya caccaki fitaccen malamin addini, Sheikh Ahamd Gumi a kan tsokacinsa, inda yace a ninke yake a cikin duhu.

Fani-Kayode yayi martani ne a kan tsokacin Gumi inda yace in har za a iya yafewa masu shirya juyin mulki, me zai sa ba za a iya yafewa 'yan binidga ba? Fani-Kayode yace

"Ta yuwu mu yiwa Hitler, Pol Pot, Stalin, King Leopard 11 na Belgium, Osama Bin Ladin, Al Bagdadi, Abubakar Shekau da duk wani wanda ya kashe mutane da yawa afuwa bayan mutuwarsu saboda tarihin da suka kafa a duniya."

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Source: Legit.ng

Online view pixel