Dakatar da Sheikh Nuru Khalid: Kungiyoyi sun yi martani masu zafi

Dakatar da Sheikh Nuru Khalid: Kungiyoyi sun yi martani masu zafi

  • 'Yan Najeriya tare da kungiyoyi masu zaman kansu sun yi martani ga gwamnati kan dakatar da Sheikh Nuru Khalid da aka yi
  • A bangaren kungiyoyin arewa, sun goyi bayan Limamnin Apo din inda suka ce Dansadau ya na da wani buri nasa da yake son cimma wa
  • CAN ta bukaci jama'a da su daina yanke hukunci har sai an gane wace yarjejniya ke tsakanin limamin da kwamitin Masallacin

'Yan Najeriya sun yi martani kan dakatar da Sheikh Nuru Khalid da aka yi daga limancin Masallacin Apo da ke Abuja.

Vanguard ta ruwaito cewa, an dakatar da Nura ne sakamakon caccakar shugaban kasa Muhammad Buhari da ya yi kan farmakin da aka kai wa jirgin kasan da ya debo fasinjoji daga Abuja zuwa Kaduna a ranar Litinin da ta gabata.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Ku hana kira fita daga dukka layukan da babu rijista - Buhari ga kamfanonin sadarwa

Dakatar da Sheikh Nuru Khalid: Kungiyoyi sun yi martani masu zafi
Dakatar da Sheikh Nuru Khalid: Kungiyoyi sun yi martani masu zafi. Hoto daga @dailytrust
Asali: Twitter

Jama'a da dama sun kushe hukuncin kwamitin Masallacin yayin da wasu kuwa suka goyi bayan hukuncin, Vanguard ta ruwaito.

Kungiyar Kiristoci ta kasa, kungiyar matasan arewa da gamayyar kungiyoyin arewa sun bayyana ra'ayoyinsu kan lamarin.

Matasan arewa

Daga Arewa, Alhaji Gambo Ibrahim Gujungu ya ce:

"Daga nan kungiyar matasan arewa, muna mutunta dukkan malaman addini. Don haka ba za mu hada barranta da Sheikh Nura Khalid ba.
"Amma kuma idan aka duba martanin jama'a, 'yan Najeriya sun fusata da kashe-kashen da ake yi marasa karewa, garkuwa da mutane da sauran miyagun al'amuran da basu karewa. Muna fatan hukumomi za su tashi tsaye kan lamarin. Fatanmu shi ne, limamin Abuja da wadanda suka dakatar da shi za su sasanta ta yadda zai cigaba da fadakarwa a watan Ramadan."

Kara karanta wannan

Farmakin jirgin kasa: Obasanjo ya yi martani kan halin da ake ciki

A yayin jawabi a madadin matasan arewa, Salihu Danlami ya ce:

"Babu shakka limamin Masallacin Apo yana da gaskiya. Hakkin kowacce gwamnati ta arziki shi ne bai wa jama'a kariya da dukiyoyinsu.
"Dukkanmu rayuwa muke a cikin tsoro, ba mu iya zuwa wasu birane a arewa maso yammacin kasar nan ta titi, jiragen sama ko jiragen kasa.
"Wannan kira ne ga Buhari da ya yi garambawul ga dukkan tsarin tsaro tare da kawo wadanda za su yi aiki saboda 'yan Najeriya."

Martanin CAN

A bangaren CAN kuwa, Rabaren John Joseph Hayab ya ce:

"Na gane cewa dakatar da limamin an yi shi ne bayan kwamitin Masallacin ya amince kuma mu ba dole mu san yarjejeniyar da ke tsakaninsu ba kafin ya fara limanci a Masallacin.
"Don haka ya dace 'yan Najeriya su kiyaye hukuncin har sai mun san abinda ya faru tare da sanin yarjejeniyar da ke tsakaninsu kafin su yanke hukunci kan lamarin."

Kara karanta wannan

'Yan Ta'adda Sun Ji Ba Daɗi Yayin Da Sojoji Suka Kashe Fiye Da 85 a Kaduna, Zamfara Da Borno

Martanin CNG

A bangaren CNG kuwa, Suleiman Abdulazeez ya ce:

"Ba na tunanin za a ce mutum ya yi laifi saboda ya duba tsarin tsaron kasar nan kuma ya bukaci gwamnati ta bai wa rayukan 'yan kasa kariya.
"Ba limamin kadai bane a wannan matsayar. Kawai dai lamarin nan ya shafi wani Dansadau ne wanda ya ke son samun wuri a mulki. Zai yuwu Dansadau ya dauka hukuncin nan saboda son kai ko rashin sani, amma babu shakka wani buri nasa yake son cikewa.
"Dansadau ya fito daga jihar Zamfara, yankin da ya bari tun bayan zamansa Sanata. Abun kunya ne ga shugabannin da ba za su iya tseratar da rayukan jama'a ba kuma su ce za su hana su magana."

Asali: Legit.ng

Online view pixel