Bayyanar dan majalisar wakilai kirji bude a majalisa ya tada kura, bidiyon ya bayyana

Bayyanar dan majalisar wakilai kirji bude a majalisa ya tada kura, bidiyon ya bayyana

  • An zargi dan majalisar wakilai, Honarabul Ifeanyi Chudy Momah da shiga zauren majalisa tsirara a ranar Alhamis da ta gabata
  • Kamar yadda daya daga cikin abokan aikinsa, Mohammed Monguno yace, Momah bai yi shigar kwarai ba kuma hakan yasa bai dace a sauraresa ba
  • Sai dai, bayan Momah ya kare kansa ta hanyar sanar da cewa kuraje gare shi, mataimakin kakaki, Idris Wase ya bukaci ya kawo takardar asibiti kan hakan

An yi wata takaitacciyar dirama a ranar Alhamis, 31 ga watan Maris a zauren majalisa tarayya yayin da ake tsaka da zama.

An tattauna ne kan shigar Honarabul Ifeanyi Chudy Momah mai wakiltar mazabar Ihiala a tarayya daga jihar Anambra, wanda aka nuna shigarsa ta saba wa tsarin shigar 'yan majalisar.

Kara karanta wannan

Sabuwar Matsala: Tsohon shugaban majalisar dokokin jiha ya yi murabus daga APC

Bayyanar dan majalisar wakilai kirji bude a majalisa ya tada kura, bidiyon ya bayyana
Bayyanar dan majalisar wakilai kirji bude a majalisa ya tada kura, bidiyon ya bayyana. Hoto daga @Ifeanyimomahmhr)
Asali: Twitter

Yadda lamarin ya fara

Dan majalisa Mohammed Monguno dan jam'iyyar APC daga jihar Borno ya ce Ifeanyi Momah bai yi shigar arziki ba kuma ya bayyana tsiraicinsa, ba za a saurare shi ba.

A kalamansa: "Honarabul Momah bai yi shigar arziki ba kuma hakan ya yi karantsaye ga dokokinmu. Saboda hakan, bai dace a sauraresa ba tunda tsirara yake."

A martanin Momah na kare kansa kan maganar Monguno, dan majalisar daga kudu maso gabas yace yana fama da kuraje ne wanda hakan yasa ya yi wannan shiga.

Ya ce: "Bani da lafiya wanda hakan yasa nake fama da kuraje kuma ina kusan shidewa. Zafi na bani wahala kuma da kyar nake numfashi idan na rufe botiran riga ta ko na saka nakatayil. Wannan al'amarin shi ne yasa zan kasa bayyana bukatar jama'ata."

Kara karanta wannan

Daga APC zuwa SDP: Ana neman mai maye gurbin dan majalisar Kwara bayan ya sauya sheka

A yayin jawabi, mataimakin kakakin majalisa, Idris Wase, ya ce: "Dokar majalisa ta bayyana cewa dole ne a yi shigar kirki. Na yarda akwai yuwuwar mutum ya fada rashin lafiya.
"Sai dai, ya dace ka kawo takardar rahoton rashin lafiya da zai baka damar zuwa majalisar babu shigar kirki kamar yadda dokokinmu suka bayyana. Don haka ba za ka yi magana ba kuma ina bukatar ka zauna."

A bangarensa, Honarabul Ado Doguwa, ya shawarci Momah da ya fayyace wa jama'a cewa gemunsa ne ke kawo kuragen ko kuma nakatayil.

Ga bidiyon a kasa:

Asali: Legit.ng

Online view pixel