Yunƙurin Kisa: Ƴan Bindiga Sun Buɗe Wa Babban Ɗan Majalisar APC Wuta

Yunƙurin Kisa: Ƴan Bindiga Sun Buɗe Wa Babban Ɗan Majalisar APC Wuta

  • Yanzu haka da jam’iyyar APC tana zaman makoki sakamakon kisan dan majalisa da aka yi yunkurin yi a ranar Alhamis, 31 ga watan Maris na 2022
  • ‘Yan bindiga sun kusa halaka wani dan majalisa na jam’iyya mai mulki a jihar ta kudu maso yamma, Akogun Olùgbenga Omole
  • Omole shugaban kwamitin labarai ne na majalisar jihar, kuma an kai masa farmakin ne a ranar Alhamis a Akure

Jihar Ondo - Honarabul Akogun Olùgbenga Omole, shugaban kwamitin labarai ne na majalisar Jihar Ondo, ya sha da kyar yayin da ‘yan bindiga suka kai masa farmaki a ranar 31 ga watan Maris.

‘Yan bindiga sun kai wa Omole wanda dan majalisa ne karkashin jam’iyyar APC farmaki inda suka dinga harbin motarsa a ranar Alhamis da dare.

Kara karanta wannan

Ana maganar rufe Majalisa domin tursasa Shugaban kasa ya tashi-tsaye kan lamarin tsaro

Yunƙurin Kisa: Ƴan Bindiga Sun Buɗe Wa Babban Ɗan Majalisar APC Wuta
Yan bindiga sun yi yunkurin halaka dan majalisar APC. Hoto: TVC News
Asali: UGC

Inda lamarin ya auku

Wanda ya tabbatar wa TVC News, ya ce mummunan lamarin ya faru ne a Akure, babban birnin jihar.

'Yan Sanda Sun Cafke Matashin Da Ke Kai Wa 'Yan Bindigan Neja Abinci

A bangare guda, Rundunar ‘yan sandan Jihar Neja ta kama wani matashi mai shekaru 20, Umar Dauda wanda ake zargin yana kai wa ‘yan ta’adda kayan abinci a jihar, The Punch ta ruwaito.

A wata takarda wacce jami’in hulda da jama’an rundunar ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun ya sanya wa hannu, an samu bayani akan yadda aka kama matashin bayan mazauna yankin sun bayar da bayanan sirri ga hukuma.

Kamar yadda takardar tazo:

“An yi kamen ne a ranar 16 ga watan Maris din 2022, da misalin karfe 11 na dare bayan samun bayanan sirri akan yadda ake yawan ganin wani mai kai wa ‘yan ta’adda kayan abinci a kauyen Kapako da ke Lapai.”

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: IBB ya gana da 'yan takarar shugaban kasa 4 daga yankin Arewa

Katsina: Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Kasuwa, Sun Yi Kisa, Sun Sace Mutane Da Dama

A wani labarin, Yan bindiga sun kashe wani treda a kasuwan Yantumaki a karamar hukumar Danmusa a Jihar Katsina a ranar Juma'a.

The Punch ta rahoto cewa yan ta'addan sun kuma raunata yan kasuwa bakwai sannan sun sace mutane da dama da ba a san adadinsu ba yayin harin.

Mai magana da yawun yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah, wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin ya ce mutum daya ne kadai aka kashe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel