Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari ya gana da Hafsoshin tsaro kan harin Jirgin ƙasa a Kaduna

Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari ya gana da Hafsoshin tsaro kan harin Jirgin ƙasa a Kaduna

  • Shugaban ƙasa Buhari ya karɓi bayanai daga hannun shugabannin tsaro game da harin jirgin ƙasa a Abuja-Kaduna
  • Bayan haka ne, shugaban ya umarce su da su gaggauta amfani da duk wata hanya domin kawo tsaro a layin dogon cikin gaggawa
  • Ya kuma jajantawa iyalan waɗan da suka rasu tare da Addu'a Allah ya tashi kafaɗun waɗan da ke kwance

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya gana da Hafsoshin tsaron ƙasar na kan harin da yan bindiga suka kai wa Jirgin ƙasa a Kaduna.

Hadimin shugaban ƙasa kan harkokin kafafen sada zumunta, Buhari Sallau, shi ne ya sanar da haka a shafinsa na Facebook.

Buhari da hafsoshin tsaro.
Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari ya gana da Hafsoshin tsaro kan harin Jirgin ƙas aa Kaduna Hoto: Buhari Sallau/Facebook
Asali: Facebook

Sallau ya ce:

"Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya gana da shugabannin tsaro kan abun da ya faru a Kaduna ranar 29 ga watan Maris, 2022."

Wannan na zuwa ne awanni bayan wasu tsagerun yan bindiga sun farmaki jirgin dake jigilar mutane daga Abuja zuwa Kaduna ranar Litinin da daddare.

Bayanai sun nuna cewa maharan sun halaka mutane da dama, har yanzun ba'a tabbatar da adadin waɗan da suka mutu ba, kuma sun sace wasu, yayin da wasu ke kwance a Asibiti.

Abun da suka tattauna

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa Hafsoshin tsaron sun yi wa Buhari bayani kan harin jirgi a hanyar Abuja-Kaduna jiya da daddare.

Shugaban rundunar sojin ƙasa, Laftanar Janar Farouk Yahaya, Hafsan tsaro na ƙasa da kuma Sifeta janar na yan sanda duk sun ziyarci wurin da lamarin ya faru.

Tuni dai hukumomin tsaro baki ɗaya suka ɗaura ɗamarar ceto Fasinjojin da ake tsammanin maharan sun yi awon gaba da su, a cewar fadar shugaban.

Buhari ya ba da umarnin gaggawa

Bayan karɓan bayanan, Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya bada umarnin gaggawa na kammala duk wasu matakan ba da tsaro da sa ido a kan layin dogon Abuja-Kaduna har ya kai ga na Legas zuwa Ibadan.

Ya kuma umarci hukumar Sufurin jiragen ƙasa ta gaggauta gyara wurin da ya lalace kuma a cigaba da aiki yadda ya dace ba tare da ɓata lokaci ba.

Kazalika ya umarci shugabannin tsaron su gaggauta dawo da Fasinjojin da aka sace, kana su tabbatar sun damke duk wani ɗan ta'adda domin ya girbi abin da ya shuka.

Ya ƙara jaddada umarnin da ya bayar tun baya cewa kada Sojoji su kuskura su raga wa yan ta'adda, sun ragargaje su babu ƙaƙƙautawa. Sannan kada su bar duk wanda ke rike AK-47 ba bisa ƙa'ida ba da ransa.

Shugaba Buhari.
Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari ya gana da Hafsoshin tsaro kan harin Jirgin ƙas aa Kaduna Hoto: Buhari Sallau/Facebook
Asali: Facebook

A sanarwan da Femi Adeshina, kakakin shugaban ya fitar, Buhari ya ce:

"Kamar kowane ɗan Najeriya, na yi baƙin ciki da abinda ya faru, karo na biyu kenan, wanda ya yi sanadin rasa rayukan mutane, wasu kuma suka jikkata."
"Wannan harin kan jirgin ƙasa, hanyar sufurin mutane ma fi sauki da aminci, mugunta ce, tunanin mu na tare da iyalan mamatan, da addua ga waɗandaa ke kwance."

A wani labarin kuma IGP da COAS Sun nufi wurin da yan bindiga suka ɗana wa Jirgi Bam a Kaduna

Shugaban yan sanda, IGP Usman Alkali Baba, da shugaban Sojojin Najeriya, Janar Farouk Yahaya, zasu je wurin da yan bindiga suka dasa Bam.

Wannan na zuwa ne bayan wasu yan ta'adda sun dasa wa Jirgin ƙasa Bam, suka bude wa Fasinjoji wuta a layin Dogon Abuja-Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel