Sifeto Janar IGP Alkali ya yi sintiri titin Abuja-Kaduna, ya zuba jami'an tsaro

Sifeto Janar IGP Alkali ya yi sintiri titin Abuja-Kaduna, ya zuba jami'an tsaro

  • Shugaban yan sandan Najeriya da kansa ya shiga sintiti titin Abuja zuwa Kaduna don tabbatar da tsaro
  • IGP Alkali hakazalika ya zuba tulin jami'an tsaro hanyar don dakile tsagerun yan bindiga masu garkuwa da mutane
  • Wannan ya biyo bayan harin Bam da yan bindiga suka kaiwa jirgin kasan Kaduna-Abuja makon da ya gabata

Abuja - Sifeto Janar na yan sanda, IGP Baba Usman Alkali, ya jagoranci sintiri na musamman zuwan titin Abuja zuwa Kaduna ranar Asabar, 2 ga watan Afrilu, 2023.

IGP Alkali tare da dinbin jami'an yan sanda sun dira titin da tsagerun yan bindiga suka addaba don ganin abin da ke gudana.

Kakakin hukumar yan sandan Najeriya CSP Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki a shafinsa na Tuwita.

Sifeto Janar IGP Alkali
Sifeto Janar IGP Alkali ya yi sintiri titin Abuja-Kaduna, ya zuba jami'an tsaro Hoto: @Princemoye1
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Sabon hari: Bayan ziyarar IGP Kaduna, 'yan bindiga sun bi gida-gida sun sace mutane 22

Prince Olumuyiwa Adejobi yace IGP Alkali ya baza jami'an tsaro masu muggan makamai don tabbatar da tsaro titin.

Yace:

"IGP Usman Alkali Baba yanzu haka ana sintiri titin Abuja-Kaduna tare da wasu manyan jami'an yan sanda domin ganin an zuba jami'ai wajen don kare rayuka da dukiya a titin."
"Ana sinitirin ne yayinda ake zuba jami'an tsaro wajen."

Shugaban UN yayi Allah wadai da harin jirgin kasan Abuja-Kaduna

Shugaban majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres yayi Allah wadai da harin da wasu tsagerun yan bindiga suka kai jirgin Abuja-Kaduna, wanda ya haddasa mutuwar mutane da yawa wasu suka jikkata sannan aka yi garkuwa da wasu.

Guterres a wani jawabi jiya, ya tura sakon ta'aziyyarsa ga iyalan wadanda abin ya shafa, ya kuma yi fatan samun lafiya ga wadanda suka jigata sannan yayi addu'ar kubutar da wadanda ke hannun miyagun.

Shugaban ya yi kira ga hukumomin tsaro da su zage damtse wajen kamo duk wadanda suke da hannu a wannan ta'addancin.

Kara karanta wannan

El-Rufai: Mun san inda 'yan bindiga suke, abu daya ne ya hana mu farmaki maboyarsu

Ya kara jaddada taimako da goyan bayan majalisar dinkin duniya ga gwamnati da mutanen Nijeria a yakin da suke yi da ta'addanci, cin zarafi da wasu laifuffuka.

Bayan haka ya kuma yi Allah wadai da harin da miyagu suka kai filin jirgin saman Kaduna ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel