Hayaniya ga muhalli: Kasar Ruwanda ta haramtawa musulmai kiran sallah da amsa-kuwwa

Hayaniya ga muhalli: Kasar Ruwanda ta haramtawa musulmai kiran sallah da amsa-kuwwa

  • Kasar Rwanda ta haramta amfani da amsa-kuwwa wajen kiran sallah a babbar birnin kasar saboda hayaniyar muhalli
  • An nemi Musulmai su dunga saka kararrawar waya domin tunawa da lokacin sallah
  • Sai dai hakan bai yiwa mutane da dama dadi ba inda suke ganin an tauye masu yancinsu na yin addini

Rahotanni sun kawo cewa kasar Rwanda ta hana amfani da amsa-kuwwa wajen kiran Sallah a Kigali, babbar birnin kasar, a kokarinta na rage abin da ta ambata da ‘hayaniyar muhalli’.

Aminiya ta rahoto cewa hukumomin kasar sun ce kiran sallah a masallatai da amsa-kuwwa ya saba dokar hana hayaniya a cikin al’umma.

Gwamnatin Rwanda ta bukaci Musulmai a kasar da su saka kararrawar waya idan har suna son tunawa da lokacin sallah.

Kara karanta wannan

Ramadan: Saudi ta ji uwar bari bayan ta nemi ta dakatar da haska sallolin dare da azumi

Hayaniya ga muhalli: Kasar Ruwanda ta haramtawa musulmai kiran sallah a amsa-kuwwa
Hayaniya ga muhalli: Kasar Ruwanda ta haramtawa musulmai kiran sallah a amsa-kuwwa Hoto: Indiatimes.com
Asali: UGC

Amma dai wasu Musulman kasar na ganin an tauye masu yancinsu na yin addini, duba da cewar ba dukka Musulmai bane suka mallaki wayar hannu.

Manufar gwamnatin dai ita ce ta inganta birnin na Kigali din ya zama daya daga cikin manyan birane a Afirka a bangaren zuba jari da yawon bude ido nan da shekaru 22 masu zuwa.

Rahoton ya kuma kawo cewa gwamnatin ta dauki matakin ne da nufin inganta birnin na Kigali ta yadda zai zama daya daga cikin manyan birane a Afirka a bangaren zuba jari da yawon bude ido nan da shekaru 22.

An bullo da manufofi masu yawa, amma bisa ga dukkan alamu na hana amfani da amsa-kuwwa wajen kiran Sallah ya fi tayar da kura.

Kara karanta wannan

Toraja: Garin da jamaa ke rayuwa da gawawwaki, suna ciyar da su tare da tufatarwa

Musulman birnin dai tuni suka fara bin umarnin, amma kuma sun soki lamirinsa, inda suka ce kamata ya yi a ce su rage sautinsu a maimakon haramta shi baki daya.

Sai dai matakin ba iya masallatai kawai zai shafa ba, saboda ko a watan da ya gabata sai da aka rufe coci-coci kusan 700, saboda saba wa umarnin.

Shugaba Buhari ya halarci taron bude Masallacin Izalah a Abuja, nan ya Sallaci Juma'a

A wani labari na daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci taron bude sabon Masallacin da kungiyar da'awa ta addinin Musulunci, Jama'atu Izalatul Bid'a Wa iqaamatus Sunna JIBWIS ta gina a birnin tarayya Abuja.

An bude Masallacin ne yau Juma'a, 25 ga Maris, 2022.

Shugaba Muhammadu Buhari ne babban bako na musamman a taron bude Masallacin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel