Ramadan: Saudi ta ji uwar bari bayan ta nemi ta dakatar da haska sallolin dare da azumi

Ramadan: Saudi ta ji uwar bari bayan ta nemi ta dakatar da haska sallolin dare da azumi

  • Ma’aikatar harkokin shari’ar musulunci ta kasar Saudi ta kawo sababbin dokoki na watan azumi
  • A wata sanarwa da aka fitar, an hana a dauki bidiyon sallolin da ake yi a harami, a haska a tashoshi
  • Daga baya sai aka ji gwamnati ta janye wannan dokar, amma ta bar sauran ka’idojin da aka kawo

Saudi Arabia – Ma’aikatar shari’a ta kasar Saudi ta bada umarnin haramta daukar bidiyo kai-tsaye a lokacin da ake yin sallah a lokacin watan Ramadan.

Rahoton da ya fito daga kafar Gulf News ya nuna cewa ma’aikatar ta hana amfani da na’urar daukar hoto wajen yi wa limamai da masallata bidiyo.

Dokar ta yi kokarin dakatar da duk wani haska bidiyon sallah a masallacin harami a kafofin yada labarai tare da hana kawo kananan yara zuwa masallaci.

Kara karanta wannan

Tsakaninmu Ne: Magidanci Ya Faɗa Wa Ƴan Sanda Yayin Da Suke Tuhumar Matarsa Da Yunƙurin Datse Masa Mazakuta

Kamar yadda muka samu labari a ranar Laraba, wannan yana cikin tsare-tsaren da gwamnatin kasar Saudi Arabiya ta zo da shi na watan azumin bana.

An kawo doka a kan rabon buda baki

Sannan ma’aikatar harkar addinai ta ce dole duk wata kungiya da ta ke neman damar raba kayan shan ruwa a lokacin azumin Ramadan ta nemi izinin ta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bugu da kari, ya zama dole kungiyoyi masu zaman kansu da ke raba abin buda baki bayan an karya azumin Ramadan su zauna da limaman harami tukun.

Kasar Saudi
Masallacin ka'aba a Makkah Hoto: AFP
Asali: AFP

Har ila yau daga cikin sababbin sharudan da ma’aikatar ta kawo shi ne ba a yarda irin wadannan kungiyoyi su wuce gona da iri da facaka wajen buda baki ba.

Abinci mai lasisi kurum za a raba a Iftar

Gulf News ta ce duk wata kungiya mai shirin raba abinci ga masu azumi ta na bukatar ta saye kayan buda bakin ne daga shagunan da gwamnati ta ba lasisi.

Kara karanta wannan

Dinbin mutane za su rasa aikin yi yayin da Naira ta kara durkushewa kasa a kasuwar canji

Kungiyoyin da za su yi aikin kiran mutane ga addini su na bukatar wani lasisi na dabam. Masu shirya abincin buda baki su na bukatar izinin jami’an tsaro.

Za a cigaba da haske salloli - Haramain Sharifain

Amma daga baya mun ji labari cewa bayan an yi ca a kan gwamnatin Saudi, ma’aikatar harkar addinai, kira zuwa ga addini da shiriya ta canza shawara.

Wata sanarwa da ta fito jiya daga shafin Haramain Sharifain ta tabbatar da cewa za a cigaba da daukar ibadan da ake yi kullum a masallatai masu alfarma.

Shahida Sanusi ta jawo abin magana

Kwanaki baya aka ji cewa Shahida Sanusi Lamido ta dura kan wasu Larabawa, ta ce su na da nunawa bakake wariyar launin fata kamar yadda ta gani a Saudi.

Babbar ‘diyar tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ta bayyana haka ne a Instagram. Daga baya ta gyara kalamanta, ta ce ba kudin goro tayi wa larabawa ba.

Kara karanta wannan

Gwamna Buni ga masu sukar APC: Taron gangami ne a gabanmu, ba ta kowa muke ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel