Toraja: Garin da jamaa ke rayuwa da gawawwaki, suna ciyar da su tare da tufatarwa

Toraja: Garin da jamaa ke rayuwa da gawawwaki, suna ciyar da su tare da tufatarwa

  • Joe Hattab ya ziyarci mutanen garin Torajan a kasar Indonesia, inda ba'a daukan mamata a matattu sai dai marasa lafiya a cikin al'umma
  • Rayuwa da 'yan uwa matattu a gida daya, sanya musu tufafi gami da nema musu abinci ba bakon abu bane a garin Torajan na Indonesia
  • Joe ya yi nazari game da bikin birne gawa, wanda ya dauki tsawon kwanaki biyar, sannan ya bada labarin abunda ya bincika

Wani mai bincike, Joe Hattab ya bar masu amfani da yanar gizo cikin mamaki, bayan ya wallafa bidiyon da ya dauka yayin ziyarar da ya kaiwa mutanen Tana Torajan a kasar Indonesia, inda rayayyu da matattu suke rayuwa tare - dabi'ar da suka dauka a matsayin al'ada.

Inda ya fara tsayawa shi ne wurin iyalin da suka rasa mahaifinsu kimanin shekara daya da ta wuce, amma ba su yi bikin birne gawarsa ba.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: 'Yan Najeriya ke son na tsaya takara, ba wai son raina bane, inji Atiku

Toraja: Garin da jamaa ke rayuwa da gawawwaki, suna ciyar da su tare da tufatarwa
Toraja: Garin da jamaa ke rayuwa da gawawwaki, suna ciyar da su tare da tufatarwa. Hoto daga Joe Hattab
Asali: Facebook

Iyalin da ba a ambaci sunansu ba, sun adana gawar mahaifinsu ta hanyar amfani da allurar hana gawa rubewa, gami da saka shi a akwatin gawa, tare da aje mataccen a gida daya dasu, amma a wani daki daban.

A akwatin gawarsa, sun saka mahimman abubuwansa, sannan sun sanya masa tufafi kamar lafiyayyen mutum. Kamar yadda Joe ya bayyana, ya gano yadda suke sama wa mataccen abinci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Iyali na biyu da ya ziyarta, wanda mahaifiyarsu ta rasu watan da ya gabata. Itama an bata kulawa ta musamman kamar yadda aka bai wa mataccen mutumin da aka ambata.

Sun yi wa marigayiyar ado cikin sutura mai kyau da yan kunnaye, tare da aje ta a daki na musamman, kafun su shirya bikin birne gawarta.

Ga iyalan duka biyu, matattun nasu ba marasa rai bane, sai dai suna ganinsu ne a marasa lafiya har zuwa sanda aka tsaida ranar birnesu.

Kara karanta wannan

'Karin bayani: Bayan watsi da kujerar da Ganduje ya bashi, Yakasai ya fita daga APC

Bikin birne mamata

Fitaccen mai bincike ya halarci kasaitaccen bikin birne mamatan, yayin da ya dauki tsawon kwanaki biyar, wanda ya kunshi jerin shagulgulan da mutane da dama basu saba gani ba, idan ba yan garin Torajan ba.

Bikin al'ada na Ma'Nene yana daya daga cikin mahimman shagulgula a al'adarsu, baya ga bikin birne gawan da suka dauka a mafi tsadan shagali a duniya.

Bidiyon mabaracin Legas dauke da bandiran kudi a jakunkuna ya janyo maganganu

A wani labari na daban, wani mabaraci ya jefa mutane da dama cikin tsananin mamaki bayan an kama shi da bandir-bandir na nairori a jakunkuna. An gano yadda kudaden ke da yawan gaske kuma sun kama tsakanin N1000 zuwa N100.

A halin yanzu bidiyon ne ke tashe a yanar gizo, wanda ke nuna makudan kudaden da mabaracin ya mallaka a jakunkunanshi.

An yi nasarar damke mabaracin, inda aka tilastashi ya zazzage dukkan jakunkunan da ya mallaka, inda aka ga kudi mai tarin yawa.

Kara karanta wannan

Budurwa ta yi watsi da saurayin da ya kashe N1m don tafiyarta UK, ya fada tashin hankali

Asali: Legit.ng

Online view pixel