Da yardar Allah ni zan gaje Buhari a 2023: Dan takaran PDP ya lashi takobi

Da yardar Allah ni zan gaje Buhari a 2023: Dan takaran PDP ya lashi takobi

  • Gwamnan jihar Ribas, ya bayyana abubuwan da yake so ya cimma idan ya zama shugaban kasa a zaben 2023
  • Ya bayyana cewa, yana da yakinin dawo da zaman lafiya kasar nan matukar aka zabe shi domin ya gaje Buhari
  • Gwamnan ya kuma bayyana cewa, Najeriya na bukatar shugaba kamarsa domin ciyar da kasar gaba da magance matsaloli

Benue - Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya ce da yardar Allah zai lashe zaben shugaban kasa na 2023 da aka sa a gaba.

Wike ya bayyana hakan ne a yayin wani taron tuntuba da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP reshen Benue a gidan gwamnati da ke Makurdi a ranar Lahadi.

Gwamnan Ribas ya sha alwashin gaje Buhari
Ba wani, ni zan lashe zaben 2023: Dan takarar shugaban kasan PDP ya lashi takobi | Hoto: punchng.com
Asali: Facebook

Hakan na zuwa ne kwana guda bayan da gwamnan na jam’iyyar PDP ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a karon farko a zabe mai zuwa, kamar yadda ya tada a Twitter.

Kara karanta wannan

Gwamna Yahaya Bello ya bayyana wanda ya kamata ya gaji Buhari a zaben 2023

Wike ya ci gaba da cewa, tare da jama'a za su aiwatar da wani tsari na hadin gwiwa don dawo da zaman lafiya da tsaro a 'yan Najeriya.

Ya kuma sha alwashin magance matsalar rashin tsaro kwata-kwata a kasar matukar ya zama shugaba a 2023.

Ba Wike kadai bane dan jam'iyyar PDP da ya bayyana aniyar tsayawa takara a zaben mai zuwa ba.

Da yake amsa tambaya kan abin da zai yi na daban ga kasar nan idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa, Gwamna Wike ya sha alwashin magance matsalar rashin tsaro da ke kara kamari a kasar.

Gwamnan wanda ya yi Allah wadai da harin ta’addancin da aka kai a filin jirgin sama na Kaduna a karshen mako, ya ce ‘yan Najeriya na bukatar shugaba mai daukar matakin gaggawa da zai magance matsalar rashin tsaro a kasar.

Kara karanta wannan

Mulki ya samu: Bidiyo ya nuna sabon shugaban APC na buga wasan dara da wani sanata

Da yake nasa jawabin, Wike ya bayar da tabbacin cewa idan aka zabe shi, gwamnatinsa za ta samar da doka da oda domin a samu karin hannayen jarin kasashen waje kai tsaye zuwa kasar.

Gwamna Yahaya Bello ya bayyana wanda ya kamata ya gaji Buhari a zaben 2023

A wani labarin, gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya bayyana cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, na bukatar dan takarar shugaban kasa wanda zai gyara albarkatun kasar ba tare da la’akari da yankin da ya fito ba.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 28 ga watan Maris, a wata hira da Channels TV yayin da ake tsaka da kira ga a mika shugabancin ga yankin kudancin Najeriya.

Ya ce: “Abin da yan Najeriya ke bukata shine kwararren dan takara, jajirtacce, mai tunani da wayo wanda zai gyara kasar ba tare da la’akari da yankin da ya fito ba.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya karyata Gwamna Fayemi, ya fadi sirrin da Shugaban kasa ya fada masu

Asali: Legit.ng

Online view pixel