Hana nuna wa duniya sallar Tarawih a Ramadana: Kungiyar Musulmai ta caccaki Saudiyya

Hana nuna wa duniya sallar Tarawih a Ramadana: Kungiyar Musulmai ta caccaki Saudiyya

  • Kungiyar MMWG ta nuna damuwarta bisa ga yadda hukumomin Saudiyya suka sauya tsarin daukar bidiyo na sallar Tarawih
  • Wannan na zuwa ne bayan da Saudiyya tace ta haramta daukar bidiyon kai tsaye tare da yada shi a watan Ramadana
  • Kungiyar ta yi kira ga kasashen musulmai a duniya da su tashi tsaye domin hana Saudiyya aiwatar da wannan manufa

Najeriya - Kungiyar Muslim Media Watch Group ta Najeriya ta ce matakin Saudiyya na hana yada sallar tarawihi kai tsaye daga masallacin Harami na Makkah da kuma masallacin Annabi Muhammad da ke Madina a cikin watan Ramadan mai zuwa sam ba daidai bane.

Kungiyar ta koka da cewa, hakan kamar killace musulman duniya ne da samun kusanci da ubangijinsu kasacewar sallar ta Tarawih na kara shajja'a musulmai da dama.

Kungiyar Musulmai ta caccaki Saudiyya ta koka kan hana yada bidiyon sallar Tarawih
Hana nuna wa duniya sallar Tarawih a Ramadana: Kungiyar Musulmai ta caccaki Saudiyya | Hoto: gulfnews.com
Asali: UGC

Hakazalika, kungiyar ta kuma nuna damuwar da cewa, nuna sallar Tarawih din ga duniya wani lamari ne da tuni mutanen duniya sun saba dashi, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kudin Paris Club: Kotu ta yi watsi da wata kara da jihohi 36 suka shigar kan gwamnatin Buhari

Yarima mai jiran gado ne ya kakaba wannan hani, MMWG

A martanin da kungiyar ta mayar kan hanin, ta yi ikirarin cewa yarima mai jiran gado na Saudiyya, Sarki Muhammad Salman ne ya sanya shi, kungiyar ta bayyana hakan a matsayin cin mutunci ga addinin Musulunci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kungiyar ta MMWG a cikin wata sanarwa da ta fitar ta hannun kodinetan ta na kasa Alhaji Ibrahim Abdullahi a ranar Lahadi, ta yi kira ga mahukuntan Saudiyya da su janye wannan umarni ba tare da bata lokaci ba.

Hakazalika, ya kara da kwatanta yada Tarawih a matsayin wani aiki na lada tsakanin bawa da Allah wanda ke habaka daidaitaccen ruhi, natsuwa da kwanciyar hankali kuma hana shi zai zama abu mafi ciwo ga duk musulmin duniya.

Don haka MMWG ta yi kira ga kungiyar kasashen musulmi ta duniya da kungiyar hadin kan kasashen musulmi da su gargadi mahukuntan Saudiyya da su kaurace wa wannan matakin da zai iya haifar mata da suka a ko da yaushe.

Kara karanta wannan

Ramadan: Saudi ta ji uwar bari bayan ta nemi ta dakatar da haska sallolin dare da azumi

Farkon batun daga Saudiyya

Idan baku manta ba, rahotanni daga kasar Saudiyya sun bayyana cewa, hukumomin kasar sun haramta daukar bidiyon sallar Tarawih kai tsaye tare da yada shi ga kafafen yada labarai a duniya.

Wannan lamari na zuwa ne kwanaki kadan ga watan Ramadana; watan da muslman duniya ke azumi tare da yawaita ibadu.

Wani rahoton da World Gulf ta fitar ya bayyana cewa, kasar ta Saudiyya ta fitar da sabbin matakai a Masallatai biyu masu daraja a kasar, ciki har da sanya ido kan abincin buda baki da wa'azi da ma shi kansa daukar bidiyon na Tarawih.

Saudiyya ta dage wasu dokokin Korona yayin da Ramadana ke karatowa

A wani labarin, kasar Saudiyya ta ce ta dauke mafi yawan takunkumin Korona da suka hada da ba da tazara yayin sallah da kebe masu shigowan da suka yi rigakafin Korona, matakan da za su iya saukakawa masu shiga kasar domin ibada.

Kara karanta wannan

Umahi Ya Ziyarci Buhari, Ya Ce Takararsa Na Shugabancin Ƙasa 'Aikin Allah' Ne

Shawarar ta ce hakan zai shafi wurare daban-daban na taro a kasar, ciki har da masallatai, in ji majiyar ma'aikatar harkokin cikin gida ta Saudiyya, kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.

Sai dai, za a bukaci mutane suke sanya takunkumin fuska a wuraren da suke rufe, bisa ga shawarar, wacce ta fara aiki ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel