Da Ɗuminsa: Ƴan Sanda Suka Kai Samame Gidan Muhuyi Rimingado a Kano, An Ji Ƙarar Harbin Bindiga

Da Ɗuminsa: Ƴan Sanda Suka Kai Samame Gidan Muhuyi Rimingado a Kano, An Ji Ƙarar Harbin Bindiga

  • Jami'an tsaro a Kano sun kai samame gidan dakataccen shugaban hukumar yaki da rashawa ta Jihar Kano, Muhuyi Rimingado
  • Makwabta sun tabbatar da cewa sun hangi motoccin jami'an tsaro misalin karfe 7 na dare sannan daga bisani an ji karar harbin bindiga
  • Abdullahi Kiyawa, mai magana da yawun yan sandan Jihar Kano ya ce bai da masaniya kan samamen amma zai bincika ya bada bayani daga baya

Kano - Yan sanda a Jihar Kano a daren ranar Lahadi sun kai samame gidan tsohon shugaban hukumar yaki da rashawa da sauraron korafin mutane, PCACC, Muhuyi Rimingado, Daily Nigerian ta rahoto.

A watan Yulin bara ne aka dakatar da Rimingado bayan fara bincike kan wasu kwangiloli da aka bawa wasu kamfanoni masu alaka da iyalan gwamna.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan Sanda Sun Cafke Ɗaya Cikin Manyan Kwamandojin Shugaban 'Yan Bindiga Bello Turji

Da Duminsa: 'Yan Sanda Suka Kai Samame Gidan Muhuyi Rimingado a Kano, An Ji Karar Harbin Bindiga.
'Yan Sanda Suka Kai Samame Gidan Muhuyi Rimingado a Kano, An Ji Karar Harbin Bindiga. Hoto: Daily Nigerian.
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daily Nigerian ta tattaro cewa yan sandan sun ajiye motoccinsu kusa da gidansa da ke Yahaya Gusau Road, suka kai masa samame misalin karfe 7 na dare.

Makwabtan Muhuyi Rimingado sun magantu kan samamen

Mazauna yankin sun tabbatarwa Daily Nigerian samamen, suna cewa sun ji karar harbin bindiga yayin da yan sandan suke kokarin kama Rimingado.

"Mun ji karar harba bindiga kuma mun ga jami'an tsaro kusa da gidan. Daga bisani misalin karfe 9.30 na dare mun ji karar gudun tayoyin mota a lokacin da suka bi sahun wata mota da ta fito daga gidan," a cewar wani makwabcin Rimingado da ya nemi a sakaya sunansa.

Amma, ba a tabbatar ko yan sandan sun kama shi ba yayin samamen.

Kakakin yan sanda Jihar Kano, Abdullahi Kiyawa ya ce ba a masa bayani ba game da lamarin, amma ya yi alkawarin zai bincika.

Kara karanta wannan

Da dumi: Jihar Kaduna ta sake daukar dumi yayin da yan bindiga suka kashe mutum 50, sun yi awon gaba da wasu

Kotu ta yi watsi da bukatar Rimingado na kada a kama shi kuma a dena bincikarsa

A ranar 1 ga watan Maris, kotun tarayya da ke Kano ta yi watsi da bukatar da Rimingado ya shigar na neman a hana Majalisar Dokokin Kano da yan sanda daga yin bincike a kansa, kama shi ko masa barazana har sai an ji hukunci kan karar da aka shigar a babban kotun jihar.

Idan za a iya tuna wa, Majalisar Dokokin Jihar Kano ta gayyaci Rimingado ya bayyana a gaban kwamitin wucin gadi da aka kafa don duba korafin da aka shigar a kansa a ranar 14 ga watan Yulin 2021.

Amma, Rimingado, yayin da ya bada uzurin rashin lafiya, ya nemi a bashi kwafin takardar korafin da aka kai wa majalisar a kansa ya nemi karin lokaci kafin ya bayyana a ganbanta.

Asibitin kasa ta ce Rimingado ya gabaarwa majalisa takardan lafiya na bogi

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kutsa har cikin gida, sun bindige Shahararren ɗan kasuwa har Lahira

A ranar 19 ga watan Yuli, Asibitin Kasa ta rubuta wa Majalisar Dokokin Kano wasika na cewa bayanan lafiyarsa da ya gabatarwa majalisar na bogi ne.

Ta bada wannan bayanin ne a ranar 19 ga watan Yulin 2021 a takarda mai lamba NHA/CMAC/GC/0117/2021/V.I/01 dauke da sa hannun direkta Dr A.A. Umar.

Asibitin na Kasa ta ce ta yi bincike game da takardun lafiyar ta kuma gano na bogi ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel