Borno: Dakarun sojin Najeriya sun gano wurin hada bama-bamai a Sambisa

Borno: Dakarun sojin Najeriya sun gano wurin hada bama-bamai a Sambisa

  • Dakarun sojin Najeriya na rundunar Operation Desert Sanity sun gano wurn kera bama-bamai a dajin Sambisa
  • Rundunar ta wallafa wannan cigaban a shafinta na Twitter inda suka kai samame sansani miyagun da ke Ukuba
  • Wannan cigaban na zuwa ne bayan sa’o’i kadan da bam ya tashi a hayin Danmani da ke karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna

Sambisa, Borno - Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta na Operation Desert Sanity sun gano wuraren da ake gudanar da aikin kera bama-bamai a dajin Sambisa dake Borno.

Rundunar ta bayyana hakan ne a ranar Asabar a wata wallafa da ta yi a shafinta na sada zumuntar zamani na Twitter.

Borno: Dakarun sojin Najeriya sun gano wurin hada bama-bamai a Sambisa
Borno: Dakarun sojin Najeriya sun gano wurin hada bama-bamai a Sambisa. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC
"A ci gaba da aikin share fage, rundunar zakakuran sojoji na Operation Desert Sanity a yau sun sake kai samame sansanin Ukuba/Camp Zairo a dajin Sambisa tare da gano wasu bama-bamai na kungiyar BokoHaram/ISWAP," in ji sanarwar.

Kara karanta wannan

An fitar da sunayen wadanda za su rike mukamai a APC, babu wasu ‘Yan takarar Buhari

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan lamarin ya zo ne sa’o’i kadan bayan da rundunar ‘yan sandan da ke yaki da dasa bama-bamai ta gano tare da dakile wani bam a unguwar Danmani da ke Rigasa a karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Hakan ya biyo bayan wasu mutanen yankin da suka jigata sakamakon fashewar wani abu a safiyar ranar Juma'a.

A cewar Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro na cikin gida na Kaduna, an ce fashewar ta faru ne bayan wani bam da aka dana a cikin babur din wani Mohammed Hassan, ma’aikacin POS a yankin ya tashi.

“Binciken farko da aka yi ya nuna cewa, Hassan ya je ya dauko babur dinsa yayin da yake bakin aiki a kusa da shagon, kuma da ya tada babur din sai ya fashe,” in ji kwamishinan.
“Bam din ya haifar da munanan raunuka ga Hassan da wani mai wucewa da har yanzu ba a san ko wanene ba. Haka kuma an samu lalacewar rufin ginin da ke kusa.”

Kara karanta wannan

Mu ya mu: ‘Yan takarar shugaban kasa na PDP sun gana don zaban daya kwakkwara

Wani abu mai fashewa ya tarwatse a hayin Danmani da ke Kaduna

A wani labari na daban, mazauna yankin Danmani na Rigasa, cikin ƙaramar hukumar Igabi dake jihar Kaduna sun shiga tashin hankali bayan fashewar wani abu a daren juma'a.

Lamarin ya auku ne, kusa da shagon P.O.S, wajen masallacin Abubakar Sadiq, kamar yadda mazauna yankin suka bayyana.

Daily Trust ta tattaro yadda aka ga wani abu mai fashewa kusa da wani babur, wanda ake tunanin mallakin mai shagon P.O.S din ne a yankin.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel