Da duminsa: Wani abu mai fashewa ya tarwatse a hayin Danmani da ke Kaduna

Da duminsa: Wani abu mai fashewa ya tarwatse a hayin Danmani da ke Kaduna

  • Mazauna yankin rigasa sun shiga ruɗani, yayin da wani abu mai fashewa ya fashe a daren Juma'a kusa da mai P.O.S, wajen wani masallaci
  • Lamarin ya ritsa da mutane uku, wanda daga cikinsu mai P.O.S din ne yafi samun matsanancin rauni, daga bisani aka garzaya dashi asibiti
  • Hakan ya faru ne, bayan wasu makonni da kwamishinan kula da lamurran cikin gida ya bukaci jama'a da su sa ido, duba da rahoton yadda ƴan ta'adda ke shirin dasa abubuwa masu fashewa a wurare

Mazauna yankin Danmani na Rigasa, cikin ƙaramar hukumar Igabi dake jihar Kaduna sun shiga tashin hankali bayan fashewar wani abu a daren juma'a.

Lamarin ya auku ne, kusa da shagon P.O.S, wajen masallacin Abubakar Sadiq, kamar yadda mazauna yankin suka bayyana.

Kara karanta wannan

Dan sanda ya halaka rayuka 2 yayin da ya yi kokarin tserewa daga masu kama shi a Bauchi

Da duminsa: Wani abu mai fashewa ya tarwatse a hayin Danmani da ke Kaduna
Da duminsa: Wani abu mai fashewa ya tarwatse a hayin Danmani da ke Kaduna. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta tattaro yadda aka ga wani abu mai fashewa kusa da wani babur, wanda ake tunanin mallakin mai shagon P.O.S din ne a yankin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani ɗan sa kan yankin, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya labarta yadda fashewar abun ya raunata mai P.O.S din, wanda daga bisani aka garzaya dashi asibiti.

"An garzaya da mutumin asibiti don nema masa lafiya, saboda kafafunsa da ƙunbunan kafafun sun samu rauni matuka. Amma, an kai wa ƴan sanda kara," a cewarsa.

Wani mazaunin yankin mai suna Shehu, ya bayyana yadda mutane uku suka samu raunuka yayin aukuwar lamarin.

A cewarsa, rundunar cire bam ta isa wurin, inda ta tsaida tashin wani abu mai fashewan.

"Daga cikin mutane ukun da suka samu raunukan, akwai mai P.O.S din wanda baya cikin hayyacin shi, sannan yana samun kulawa a asibitin 44, inda sauran mutane biyu suka samu kananan raunuka," a cewarsa.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Yan bindiga sun kashe babban Basarake a kan hanyar zuwa gaida mara lafiya

Sai dai, gwamnatin jihar da ƴan sandan jihar har yanzu ba su yi tsokaci game da lamarin ba. Kakakin rundunar, ASP Jalige Mohammed, bai amsa kiran wayar da aka yi masa ba.

Daily Trust ta ruwaito yadda fashewar abun yazo wasu makonni bayan gwamnatin jihar ta bakin kwamishinan kula da lamurran cikin gida, Samuel Aruwan, ta ja kunnen mazauna yankin da su zama masu sa ido, saboda ƴan ta'adda na shirin dasa abubuwa masu fashewa a makarantu, kasuwanni da wuraren bauta.

Gwamna El-Rufai ya ɗage dokar hana fita da ya saka a LG 2 na Kaduna

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Kaduna ta cire dokar ta ɓacin awa 24 da tasa a kananan hukumomin Kaura da Jema'a na jihar Kaduna bisa karya dokar da yankin suka yi.

Daily Trust ta ruwaito cewa, hukuncin cire dokar yazo ne bayan dubi da rahoton halin tsaron yankin da jami'an tsaro suka gabatar wanda ya bada tabbacin zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Daukar fansa: Fusatattun matasa sun far wa matafiya a wani yankin Kaduna

Kwamishinan kula da tsaro da lamurran cikin gida, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a wata takarda da ta fita a ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel