An fitar da sunayen wadanda za su rike mukamai a APC, babu wasu ‘Yan takarar Buhari

An fitar da sunayen wadanda za su rike mukamai a APC, babu wasu ‘Yan takarar Buhari

  • Ana tunani jerin wadanda Gwamnoni suke goyon baya a zaben shugabannin APC na kasa ya bayyana
  • Sanatan Abdullahi Adamu ne wanda kan Gwamnonin APC ya hadu a kan ya rike shugabancin jam’iyya
  • Amma alamu na nuna cewa babu sunan wasu wadanda ake tunanin shugaban Najeriya ya na tare da su

Abuja - Rahotanni su na nuna cewa jerin wadanda za su iya samun mukamai a majalisar NWC a jam’iyyar APC sun bayyana a ranar Asabar dinnan.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa an ware wadanda ake so su dare kan kowace kujera a zaben da za ayi yau. Kujeru fiye da 50 ake takara a kansu a APC.

Jaridar Daily Trust ta c a wannan jerin da aka fitar dazu, Sanata Abdullahi Adamu ne aka yi ittifaki a kan ya zama shugaban jam’iyyar APC na kasa.

Kara karanta wannan

Ana daf da zaben shugabannin APC, Buhari ya hadu Tinubu da wadanda suka kafa jam’iyya

Sanata Iyiola Omisore daga jihar Osun ne aka yi na’am ya zama sabon sakataren jam’iyyar APC.

Har ila yau Sanata Abubakar Kyari ne zai zama mataimakin shugaban jam’iyya na Arewa, takwaransa daga yankin Kudu zai zama Cif Emma Eneukwu.

Adamu mutumin Nasarawa ne, Kyari da Eneukwu fun fito daga jihohin Borno da Enugu. Hakan na zuwa ne bayan an ji Rt. Hon. Yakubu Dogara ya janye takara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gangamin APC
Taron APC na kasa Hoto: @bashahmad
Asali: Facebook

Kamar yadda muka samu labari, gwamnonin jam’iyyar APC 22 sun sa hannu a takardar da aka fitar da ita na sunayen ‘yan takarar da za a iya zaba an jima.

Ina mutanen Shugaban kasa?

Wata majiya ta bayyana cewa Abdullahi Adamu ne kadai ya sha a cikin ‘yan takarar da ake tunanin shugaban kasa Muhammadu Buhari yana marawa baya.

Kara karanta wannan

Taron gangamin APC: Gobe Juma'a muke shirin sakin sunayen wadanda muka zaba, Ahmad Lawan

Idan aka tafi a haka kuwa, alamu na nuna Sanata Ken Nnamani da Hon. Farouk Adamu Aliyu ba za su zama mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa ba.

A jerin, babu sunan Ife Oyedele wanda ake tunanin yana da goyon bayan fadar shugaban kasa. A baya an ji cewa Oyedele ya dade yana tare da Buhari a siyasa.

Irinsu Salihu Lukman da Victor Gaidom sun shiga cikin jerin a matsayin shugabanni na kananun shiyyoyi yayin da aka nemi sunan Ismail Ahmed aka rasa.

Betta Edu da ake tunanin an yi waje da ita, za ta iya zama shugabar mata ta APC, sannan kuma kan gwamnonin APC bai hadu a kan Ismail Buba Ahmed ba.

Jerin da aka fitar

Ragowar wadanda aka fitar da sunansu kamar yadda TVC suka rahoto sun hada da:

Festus Fuanter

Muhazu Bawa Rijau

Dr. Ijeoma Arodiogbu

D. I kekemeke

Ahmed El-Marzuk

Uguru Mathew Ofoke

Kara karanta wannan

Babu yadda gwamnonin APC suka iya, sun goyi bayan wanda Buhari ke so a zaben jam'iyya

Bashir Usman Gumel

Suleiman M Argungun

F. N. Nwosu

Barr. Felix Morka

Abubakar Maikafi

Dr. Betta Edu

Abdullahi Dayo Isreal

Tolu Bankole

Ibrahim Salawu

Hon. Omorede Osifo

Matsayar Gwamnonin Yarbawa

A baya mun kawo maku labari cewa Gwamnonin kudu maso yammacin Najeriya da ke karkashin APC mai mulki sun nuna ba su tare da fadar shugaban kasa.

Gwamnonin APC sun bayyana wannan ne a wani jawabi da suka fitar ta bakin Donald Ojogo. Daga baya Buhari ya yi zama na musamman da duka gwamnonin APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel