Sabon Salo: Masu Garkuwa Sun Karɓi Giya, Taba Sigari Da Taliya Matsayin Kuɗin Fansa

Sabon Salo: Masu Garkuwa Sun Karɓi Giya, Taba Sigari Da Taliya Matsayin Kuɗin Fansa

  • Masu garkuwa da mutane sun sako wani bawan Allah da suka sace a Jihar Ekiti bayan iyalansa sun biya fansa da giya, sigari, taliya da kudi
  • Wata majiya daga yan uwan mutumin ta ce da farko Naira miliyan 2 aka nema su biya, daga bisani aka rage musu zuwa N750,000 amma da giya, sigari, taliya da wasu kaya
  • Kakakin yan sandan Jihar Ekiti Sunday Abutu, ya tabbatar da sakin mutumin amma ya ce ba shi da masaniya kan biyan kudin fansan

Jihar Ekiti - Wasu da suka yi garkuwa da wani mutum mai matsakaicin shekaru, Idowu a Jihar Ekiti sun sako shi bayan an biya su N750,000 da giya, taba sigari da taliya.

An kama wanda abin ya faru da shi ne aka yi garkuwa da shi a kan hanyar Ikole-Ijesa Isu a karamar hukumar Ikole misalin karfe 6.30 na yamma, rahoton Nigerian Tribune.

Kara karanta wannan

Da dumi: Jihar Kaduna ta sake daukar dumi yayin da yan bindiga suka kashe mutum 50, sun yi awon gaba da wasu

Sabon Salo: Masu Garkuwa Sun Karɓi Giya, Taba Sigari Da Taliya Matsayin Kuɗin Fansa.
Masu Garkuwa Sun Karɓi Giya, Taba Sigari Da Taliya Matsayin Kuɗin Fansa. Hoto: The Nation.
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Saturday Tribune ta tattaro cewa, an sako mutumin, mai wani wurin shakatawa a karamar hukumar, a safiyar ranar Juma'a a wani daji kusa da unguwar.

A cewar wata majiya, masu garkuwar sun kira yan uwansa sun nemi Naira miliyan 2 kafin suka rage kudin zuwa N750,000. Majiyar ta kara da cewa yan bindigan sun kuma karbi giya, sigari, taliya da lemun kwalba da wasu kayayyakin.

"Da farko sun nemi Naira miliyan 2 amma bayan rokonsu, sun karbi N750,000 daga iyalan. Sun karbi wasu kayayyaki kamar giya, tabar sigari, lemun kwalba, taliya kafin suka sako dan uwan mu a yau (Juma'a).," in ji majiyar.

Da aka tuntube shi, mai magana da yawun yan sandan jihar, Sunday Abutu, ya tabbatar da sakin mutumin amma ya ce ba shi da masaniya kan biyan kudin fansan.

Kara karanta wannan

Ban Damu Da Tsige Ni Da Kotu Ta Yi Ba Ko Kaɗan, Har Ƙiba Da Kyau Na Ƙara, Gwamna Umahi

Kakakin rundunar yan sandan ya ce an ceto wanda aka yi garkuwa da shi ne saboda kokarin yan sanda, vigilante da Amotekun a jihar.

Ban Taɓa Sanin Garkuwa Da Mutane Laifi Bane Har Sai Da Hukuma Ta Damƙe Ni, Shugaban Ƴan Bindiga, Surajo Mamman

A wani rahoton, Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama wani jagoran ‘yan bindiga wanda da kan shi ya bayyana yadda ya halaka kuma ya yi garkuwa da mutane da dama kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito.

Dan bindigan, Surajo Mamman wanda aka fi sani da ‘Kutaku’ mai shekaru 50 da haihuwa ya bayyana cewa shi ne na biyu daga Sani Muhidinge, dan bindigan da gwamnati take nema ido rufe.

Mahinde ya boye ne a dajin Rugu dake tsakanin jihar Katsina da jihar Zamfara. Jami’an tsaro sun tafi da shi har hedkwatar ‘yan sanda a ranar Laraba a gaban manema labarai.

Kara karanta wannan

Dan ta'adda ya gudu daga hannun hukuma yayinda aka kaishi kotu

Asali: Legit.ng

Online view pixel