Ban Damu Da Tsige Ni Da Kotu Ta Yi Ba Ko Kaɗan, Har Ƙiba Da Kyau Na Ƙara, Gwamna Umahi

Ban Damu Da Tsige Ni Da Kotu Ta Yi Ba Ko Kaɗan, Har Ƙiba Da Kyau Na Ƙara, Gwamna Umahi

  • Gwamnan Jihar Ebonyi, ya ce bai damu da hukuncin da kotu ta yi masa ba, na tsige shi daga kan kujerar sa ta gwamna
  • An samu rahoto akan yadda kotun ta tsige Umahi da mataimakinsa, Eric Igwe akan sauya shekar su daga PDP zuwa APC
  • Yayin bayani a ranar Laraba bayan kammala taro da Buhari, ya ce bayan tsige shi, har kiba da kyau ya kara kamar yadda kowa ya ke gani

FCT, Abuja - David Umahi, gwamnan Jihar Ebonyi ya ce bai damu da hukuncin da kotu ta yanke ba na kwanan nan wanda ta tsige shi daga mukaminsa na gwamna.

The Cable ta ruwaito yadda babbar kotun da ke zama a Abuja ta tsige Umahi da mataimakin sa, Eric Igwe akan sauya shekar da suka yi daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Kara karanta wannan

Umahi Ya Ziyarci Buhari, Ya Ce Takararsa Na Shugabancin Ƙasa 'Aikin Allah' Ne

Ban Damu Tsige Ni Da Kotu Ta Yi Ba Ko Kaɗan, Har Ƙiba Da Kyau Na Ƙara, Gwamna Umahi.
'Kwace Min Kujera Da Kotu Ta Yi Ko Kadan Bai Ɗaga Min Hankali Ba, Ƙara Ƙiba Ma Na Yi, Umahi. Hoto: The Cable.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A ranar Laraba bayan kammala taro da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Abuja, gwamnan Jihar Ebonyi ya ce hakan ya ci karo da kundin tsarin mulkin Najeriya tun farko.

Umahi ya ce ko a jikinsa

Kamar yadda The Cable ta bayyana, gwamnan ya shaida cewa:

“Ban damu ba saboda babu wani wuri a kundin tsarin mulki da ya nuna cewa za a iya yin karar gwamna. Don haka ba a iya kara ta.
“Sai dai hukuncin kotu, hukunci ne. Ba ina kalubalantar shi bane, amma zan iya magana akan shi don kundin tsarin mulki ya nuna cewa da zarar an zabe ka, kana da kariya.
“Kamar yadda kotun koli ta ce, duk kuru’un da aka kada, na dan takara ne. Shiyasa akwai takardun da ake so dan takara ya mallaka ba wai jam’iyya ta mallaka ba. Don haka ban damu ba.

Kara karanta wannan

Shugabancin APC na kasa: Mika kujera wata shiyya ba ka'ida bane, Abdülaziz Yari

“Ubangiji ne ya bayar da iko don in samu damar zuwa wuraren da ban je na yi kamfen din takarar shugaban kasa ba. Na kula ‘yan Najeriya suna so na kuma kila hakan ne dalilin cire ni.”

Gwamnan ya ce ya kara kyau da kiba yanzu da aka sauke shi

Ya yi godiya ga PDP inda ya ce wadanda suka soki Jesus, da sun san zai zo da ceto da ba su yi masa hakan ba.

Ya kuma bayyana cewa bai damu ba don kundin tsarin mulki ya fayyace komai kuma ya san kotu ta san komai.

Ya ci gaba da cewa

“Kun gani, cikin lokaci kankani har kiba da kyau na kara.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel