Ban Taɓa Sanin Garkuwa Da Mutane Laifi Bane Har Sai Da Hukuma Ta Damƙe Ni, Shugaban Ƴan Bindiga, Surajo Mamman

Ban Taɓa Sanin Garkuwa Da Mutane Laifi Bane Har Sai Da Hukuma Ta Damƙe Ni, Shugaban Ƴan Bindiga, Surajo Mamman

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama wani kasurgumin dan bindiga, Surajo Mamman wanda aka fi sani da Kutaku
  • Kataku ya dade a harkar halaka jama’a da kuma garkuwa da su kamar yadda da bakin sa ya bayyana ranar Laraba
  • A cewarsa, be san yawan jama’an da ya halaka ba kuma bai taba sanin babu kyau harkar da yake yi ba

Katsina - Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama wani jagoran ‘yan bindiga wanda da kan shi ya bayyana yadda ya halaka kuma ya yi garkuwa da mutane da dama kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito.

Dan bindigan, Surajo Mamman wanda aka fi sani da ‘Kutaku’ mai shekaru 50 da haihuwa ya bayyana cewa shi ne na biyu daga Sani Muhidinge, dan bindigan da gwamnati take nema ido rufe.

Kara karanta wannan

Abun mamaki: Bidiyo da hotunan yadda Firayim ministan Ethiopia ya koma 'direban' Buhari

Ban Taɓa Sanin Garkuwa Da Mutane Laifi Bane Har Sai Da Hukuma Ta Damƙe Ni, Shugaban Ƴan Bindiga, Surajo Mamman
Shugaban Ƴan Bindiga, Surajo Mamman. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mahinde ya boye ne a dajin Rugu dake tsakanin jihar Katsina da jihar Zamfara.

Jami’an tsaro sun tafi da shi har hedkwatar ‘yan sanda a ranar Laraba a gaban manema labarai.

A cewar sa bai san yawan rayukan da ya halaka ba

Kutaku ya amsa laifin sa inda ya ce:

“Na dade ina harkokin garkuwa da mutane da sauran manyan laifuka. Ba zan iya tuna yawan mutanen da nayi garkuwa da su ko kuma na halaka ba saboda su na da yawa sosai.
“Gaskiya ban ga illar abinda nake yi ba tsawon lokaci har sai da jami’an tsaro su ka kama ni. Amma yanzu ido na ya bude.”

Kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito, ya kara da bayyana yadda yake da hannu dumu-dumu a garkuwa da mutane da satar shanaye a kauyakun Dan Musa, Safana, Dutsinma da karamar hukumar Batsari dake jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Ganduje, Amaechi, Ikweremadu, wasu mutum 22 da suke cin taliyar siyasa tun 1999 har yanzu

An dakatar da layukan wayoyi daga aiki a akalla kananun hukumomi 13 na jihar Katsina don ganin bayan ta’addanci.

Cikin kananun hukumomin da ta’addanci ya shafa sun hada da Sabuwa, Faskari, Dandume, Batsari, Danmusa, Kankara, Jibia, Safana, Dutsinma da Kurfi wadanda suke kusa da dajin Ruggu inda ‘yan ta’addan suke boyewa.

Sauran kananun hukumomi 3 sun hada da Funtua, Bakori da Malumfashi.

Hotunan Mutane 5 Masu Garkuwa Da Mutane Da Ƙwararrun Mafarauta Suka Kama a Kogi

A wani labarin daban, kwararrun mafarauta a karamar hukumar Okehi a jihar Kogi sun yi nasarar kama mutane biyar 'yan kungiyar masu garkuwa da mutane, LIB ta ruwaito.

An kama mutane biyar din da ake zargi a safiyar ranar Talata a Atami, wani gari da ke wajen Osara a ranar Talata, 27 ga watan Satumban shekarar 2021.

King Habib, babban hadimi ga shugaban karamar hukumar Okehi a bangaren watsa labarai, Hon Abdulraheem Ohiare Ozovehe ya tabbatar da kama wadanda ake zargin, yana mai cewa tawagar sun dade suna adabar mutane a titin Okene-Lokoja da Okene-Auchi a jihar Kogi State.

Kara karanta wannan

El-Rufai zai rusa dubunnan gidaje a Garin Zaria, Gwamnati za ta tada Unguwa sukutum

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel