Daukar fansa: Fusatattun matasa sun far wa matafiya a wani yankin Kaduna

Daukar fansa: Fusatattun matasa sun far wa matafiya a wani yankin Kaduna

  • Rikici ya barke a wani yankin jihar Kaduna yayin da wasu matasa suka fusata suka tare hanya a yankin
  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, matasan sun kashe wani mutum da bai ji ba bai gani ba a yayin rikicin
  • Rahoton ya kuma bayyana cewa, matasan sun tada rikici ne da sunan daukar fansan harin da aka kai a yankin

Kafanchan, Kaduna - Ana zaman dar-dar a garin Kafanchan; hedikwatar Kudancin Kaduna, inda wasu fusatattun matasa a garin Maraban Kagoro da ke karamar hukumar Kaura suka tare hanya, inda suka far wa matafiya.

An ce fusatattun matasan suna ramuwar gayya ne kan wani harin da ya afku a yammacin Lahadi, inji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Rashin wutar lantarki ce matsala mafi girma ga cigabar kasar nan, Tinubu

Fusatattun matasa sun farmaki mazauna Kafanchan
Da dumi-dumi: Fusatattun matasa sun far wa matafiya a wani yankin Kaduna | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

An tattaro cewa matasan sun jibge tayu a kan hanya inda suka far wa wasu da ba su ji ba ba su gani ba, lamarin da ya yi sanadin mutuwar wani mutum mai suna Dan Asabe, mazaunin Kafanchan.

An rufe makarantu da shaguna da sauran wuraren kasuwanci a garin Kafanchan sakamakon harin.

A baya an ce wasu ‘yan bindiga sun kai hari Agban na Maraban Kagoro da ke kan titin Gidan Waya a karamar hukumar Kaura da Yammacin Lahadi.

Maharan sun kai farmaki yankin ne da misalin karfe 9:15 na dare, a cewar wata majiya, inda suka fara harbe-harbe.

Ya zuwa yanzu dai ba a samu jin ta bakin mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ba.

Ku saki Obiano komu mamaye Hedkwatarku tsirara, Matan Anambra sun ja kunnen EFCC

Kara karanta wannan

Yan Boko Haram sun sace Likita daya tilo dake asibitin Gubio, jihar Borno

A wani rahoton, wata kungiyar mata a jihar Anambra, ta yi barazanar mamaye hedkwatar hukumar EFCC dake Abuja ba tare da kaya a jikin su ba.

Punch ta rahoto cewa kungiyar mai suna, 'Anambra-North Women Empowerment Movement' ta yi barazanar ne matukar hukumar yaƙi da cin hanci ta ƙi sako tsohon gwamnan Anambra, Willie Obiano.

Kungiyar ta yi Allah wadai da wani Bidiyo dake yawo a kafafen sada zumunta, wanda aka ga Obiano na shan ruwa a Ofishin EFCC da yake tsare.

A wata sanarwa da kungiyar ta raba wa yan jarida a Awka, ranar Litinin, shugabar kungiyar Uju Ifunanya Edochie, ta zargi EFCC da nuna tozarci.

Kotu ta kwace kujerun wasu yan majalisa 20 saboda komawa APC

A wani labarin, babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja, ta sallami wasu mambobin majalisar dokokin jihar Cross River su 20 a ranar Litinin, 21 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Kungiyar Izala ta rabawa yan gudun Hijra da matsalar tsaro ta shafa a Neja kayayayyki

Kotu ta kwace kujerun su ne saboda sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa jam’iyyar All Progressive Congress (APC) mai mulki.

Kotun, a wani hukunci da mai shari’a Taiwo Taiwo ya yanke, ya riki cewa ya zama dole yan majalisar su sauka daga kujerunsu kasancewar sun yi watsi da jam’iyyar da ta dauki nauyin kawo su kan mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel