Da ɗuminsa: Gwamna El-Rufai ya ɗage dokar hana fita da ya saka a LG 2 na Kaduna

Da ɗuminsa: Gwamna El-Rufai ya ɗage dokar hana fita da ya saka a LG 2 na Kaduna

  • Gwamnatin jihar Kaduna ta cire dokar ta ɓacin awa 24 da tasa a kananan hukumomin Kaura da Jema'a bisa karya dokar da yankin da jamaa suka yi
  • Hukuncin cire dokar yazo ne bayan dubi da halin tsaron da aka samu bayan karbar rahoton tsaro daga jamiai da gwamnati ta yi
  • Kwamishinan kula da tsaron tare da lamurran gida, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a wata takarda da ta fita a ranar Alhamis

Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna ta cire dokar ta ɓacin awa 24 da tasa a kananan hukumomin Kaura da Jema'a na jihar Kaduna bisa karya dokar da yankin suka yi.

Daily Trust ta ruwaito cewa, hukuncin cire dokar yazo ne bayan dubi da rahoton halin tsaron yankin da jami'an tsaro suka gabatar wanda ya bada tabbacin zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Gwamna Tambuwal ya gana da IBB da Abdulsalami, ya bayyana shirin ‘yan takarar PDP

Da ɗuminsa: Gwamna El-Rufai ya ɗage dokar hana fita sa ya saka a LG 2 na Kaduna
Da ɗuminsa: Gwamna El-Rufai ya ɗage dokar hana fita sa ya saka a LG 2 na Kaduna Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Kwamishinan kula da tsaro da lamurran cikin gida, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a wata takarda da ta fita a ranar Alhamis.

Kamar yadda ya bayyana wannan cigaban, za'a bar kaiwa da komowa a yankunan daga 6:00 na safe zuwa 6:00 na yamma a kowacce rana, Daily Trust ta ruwaito.

"Gwamnati na burin jaddada dokar ta ɓacin da ta ayyana na tsawon awanni 24 don tsaida tarzoma.
"Za'a cigaba da sa ido. Idan tsaro ya bukaci tabbatar da hakan, gwamnati ba za tayi ƙasa a guiwa wajen mayar da dokar ta ɓacin ba," a cewarsa.

Gwamna El-Rufai ya sanya dokar hana fita a Jema'a da Kaura a jiharsa

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Kaduna ta sanya dokar hana fita hana fita a kananan hukumomin Jema’a da Kaura biyo bayan samun bayanai na shawari daga hukumomin tsaro na jihar.

Kara karanta wannan

Ku dawo mana da silalla, majalisar wakilai ta bukaci bankin CBN

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-rufai ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar ta shafinta na Twitter.

Sanarwar ta ce:

"Biyo bayan shawarwarin hukumomin tsaro, KDSG ta sanya dokar hana fita na sa’o’i 24 a kananan hukumomin Jema’a da Kaura tare da fara aiki nan take. Hakan na nufin taimakawa jami’an tsaro wajen daidaita al’amura a yankunan, da ceton rayuka da dukiyoyi da kuma ba da damar maido da doka da oda."

Asali: Legit.ng

Online view pixel